Gwamnatin Kaduna Ta Amince Da N54m Don Yin Ayyuka A Karamar Hukumar Kaura

0
701

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNATIN jihar Kaduna ta amince da naira miliyan 54 domin gudanar da sabbin ayyuka daban-daban a karamar hukumar Kaura, a cewar Bege Katuka, Shugaban yankin.

Katuka ya bayyana cewa ayyukan da za a gudanar sun hada gine-ginen famfon tuka-tuka, kwalbati, da kuma gyare-gyaren hanyoyi a yankunan karkara.

Ya sake ba mutanen yankin tabbacin jajircewa domin cika masu bukatunsu, inda ya bukaci da su mara masa baya da bashi hadin kai domin tabbatar da nasarar manufofi da shirye-shiryensu.

Shugaban karamar hukumar ya kuma bukaci mutanen, musamman manoma da makiyaya, da su guje ma ayyukan da ka iya haddasa rashin zaman lafiya, duba ga cewa lokacin noma yayi.

Ya bayyana cewa hukumar za ta gudanar da taron gari nan bada jimawa ba inda masu ruwa da tsaki za su tattauna kan ci gaban da aka samu zuwa yanzu.

“Makasudin shirin shine jin ra’ayoyin jama’a. Yana da matukar muhimmanci sannin halin da suke ciki da ra’ayoyinsu. Wannan shine abunda muke son yi,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here