‘Yan Sandan Jihar Ribas Sun Kashe Mutum 6 Dake Sace Mutane

0
644

Musa Muhammad kutama, Daga kalaba.

RUNDUNAR ‘yan sandan jihar ribas ta yi nasarar kashe wasu mutum shida da ake zargi da masu sace ,mutane ne don suyi garkuwa dasu domin karbar kudin fansa   .

Da yake sanarwa manema labarai a fatakwal nasarar da rundunar ta samu, kwamishinan ‘yan sandan jihar Usman Balele yace a wani  samame da jami’an rundunar takai ne a  maboyar masu sace mutanen dake Eneka yankin karamar hukumar Obio/Akpor jihar ribas aka yi musayar wutar har mutum shidan suka mutu”.

Ya ci gaba da cewa ko da masu sace mutanen sukayi arba da ‘yan sandan su, sai suka bude musu wuta har suka jiwa mutum biyu rauni  daga cikin ‘yan sandan a dauki ba dadin da suka yi.

A cewar kwamishinan, yayin da ‘yan sandan suka dauke su zuwa asibitin koyarwa na jami’ar fatakwal, likitoci sun tabbatarwa jami’an ‘yan sandan cewa duka mutanen biyar sun mutu.

Harwayau, rundunar ta ce ta kama wasu mutum sha biyu daga cikin masu laifin da ake zargin su da aikata laifin tayar da hankalin jama’a da fitina.

Rundunar ta samu wadanda ake zargin da miyagun makamai da suka hada da bindiga kirar AK-47. Sauran kayan laifin sune bindiga mai sarrafa kanta guda uku, Adduna guda takwas tare da tarin albarusai a wurin su da aka kama su dasu.

Kwamishinan ya kara da cewa akwai wani mai suna Ntuariuwa da ya addabi jihar da sace mutane ana yin garkuwa dasu domin neman kudin fansa wanda shima a wancan artabun anji masa mummunan rauni wanda yayi sanadiyar mutuwarsa wanda shi ne cikon mutum na shida da aka kashe.

A Karshe, rundunar ta bayyana cewa yanzu haka ta cafke wasu mutum ashirin da suka addabi ribas da aikata miyagun halaye kana ana tsare dasu don yin bincike akan su kuma dazarar an gama kotu za’a mika su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here