Gara Ta Yi Sanadin Mutuwar Yan Biyun Bakwaini A Asibitin Jihar Kuros Riba

0
1050

Musa Muhammad kutama, Daga kalaba.

GARA ta gaigaye wasu jarirai tagwaye , bakwaini biyu a karamin asibitin Obubra dake karamar hukumar Obubra ta Jihar kuros Riba.

Lamari da ya faru a asibitin sha katafi wanda ya baiwa mafi yawancin al’umma mamakin da ake zargin Garar ta kutsa kai ne zuwa dakin ajiye marasa lafiya na gaugawa dake asibitin a yayinda mahaifiyar jariran nakuda ta kamata ta haihu a asibitin.

Wakilin mu yabi diddigin labarin ta binciko yadda abin ya faru a wannan gari wata majiya data bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa wannan jarida cewa matar ta haifi bakwainin ne a sanadiyar fada da sukayi da wata makwabciyar ta dukda tana sane da cewa tana dauke da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe taje tayi fadan.

Haka kuma makwabciyar matar data haifi bakwanin mai suna Antonia ta shaidawa cewa “lokacin da ta haifi jariran tagwaye kai tsaye aka garzaya aka fadawa daraktan asibitin wanda shine jami’in kula da kiwon lafiya matakin  farko Dokta Betta Edu na jihar inda baiyi wata-wata ba ya bayar da umarnin akai maijegon da jariran ta dakin rainon jarirai bakwaini”.

Antonia ta ci gaba da cewa “maimakon subi umarnin daraktan na kai maijego da ‘ya’yan ta wancan wuri na rainon jarirai bakwaini saboda inda aka fara ajiye su asibitin bashi da kayan aiki na zamani da dakin da ake sanya jarirai bakwaini, sai suka yanke shawarar kai su wani asibiti mai zaman kansa a Ikom wanda a sanadiyar haka ne aka ce gara ta shiga ta ciji jariran bayan an ga alamar cizo a jikin daya daga cikin su  kafin ya mutu washe gari ayayin da shi ma dayan washe gari ya mutu a wannan asibiti”.

Majiyar labarin mu ta bayyana cewa shi wancan asibiti na Obubra shi ne wanda bashi da kayan aiki irin na zamani wanda kuma a can ne garar ta gwaiguyi yaran kafin daga bisani a kawo su asibitin Ikom.

Da yake yiwa wakilin mu na kudanci karin bayani Darakta janar na asibitin kula da lafiya a matakin farko Dokta Edu ya ce “lokacin da aka kawo matar asibitin kuma nasan bamu da kayan aiki, kaitsaye sai aka kai su Ikom wani asibiti mai zaman kansa wanda anan take na cire kudi naira dari biyu na basu da kuma wasu kayan jarirai gudunmuwa tunda mijin matar yaki ya
bayar da ko sisin kwabo.

Ya ce “da kudin aljihuna na cire na sayi janareto sabo na ba asibitin su kunna domin basu da wuta saboda ceton ran maijego da jariranta, amma mai makon da hakan ta faru a sanarwa kodinetocina na yankin sai suka ki suka yi son ran su na basu kudin da zasu sayi mai su zubawa janareton na kawo kudin na biya su na sallamar su da ga asibitin don dai kawai kada a samu cikas.”

Karshe dokta Betta Edu ya bayyana cewa an nada kwamitin da zai binciko musu yadda aka yi wannan sakaci don wannan shi ne na farko tarihin jihar kuros riba da aka haifi bakwaini gara ta gwaguye su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here