Mawaka Suna Kokari Wajen Isar Da Sakonni Ga Al’umma – Mashkoor M Inuwa

0
889

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

WANI matashin mawaki Mashkoor M. Inuwa Dungurawa yace mawaka suna isar da  sakonni ga al’umma cikin wakokin da suke yi kuma a harsuna daban-daban tun lokaci mai tsawo.

Mawakin, ya yi wannan tsokacin ne a cikin wata hirar da suka yi da wakilinmu a dakin sa na shirya wakoki, inda kuma ya sanar  da  cewa ko shakka babu mawaka suna bada gagarumar gudummawa wajen bayyana wasu muhimman al’amura wadanda zasu kawo amincewa cikin zukatan al’umma domin aiwatar da  abubuwa na ci gaban kasa.

Haka kuma ya bayyana cewa aikin mawaka yana da yawan gaske, sannan su kansu  al’umma sun kasance masu sauraron irin  baitukan da mawaka keyi a lokuta daban-daban wadanda suke amfani dasu wajen daukar muhimman bayanai dake tafiya a  tsarin zamantakewar yau da kullum.

Mawaki Mashkoor Dungurawa ya sanar  da  cewa ya yi wakoki masu yawan gaske wadanda suka isar da muhimman sakonni ga al’umma tun lokaci mai tsawo, tare da yin fatan alheri ga daukacin mawakan kasarnan bisa kokarin da suke yi wajen kawo sauyi cikin zamantakewar al’umma, sannan yace  yanzu haka ya yi nisa wajen fitar da wasu wakoki domin fayyace yadda rayuwa ta ke gudana a wannan karni.

A karshe, mawakin ya bayyana cewa ” duk mai bukatar ganawa dashi sai  ya ziyarce shi a katafaren dakin sa na shirya wakoki dake  layin kanikawa garin Dungurawa cikin yankin karamar hukumar Dawakin Tofa ko kan  wannan lambar waya: 07085520709.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here