Matse Wasu Jarirai 3 A Layin Karbar Fom na APPEALS, Ya Yi Sanadin Mutuwarsu

0
700

Isah Ahmed, Daga Jos.

A SAKAMAKON bin layin karbar fom din shirin tallafin noma da kiwo na hadin gwiwar bankin duniya da gwamnatin tarayya ta keyi mai suna APPEALS, a harabar ofishin shiya na hukumar bunkasa harkokin noma, ta Jihar Kaduna da ke garin Sabon birni a Karamar Hukumar Lere, an matse wasu jarirai uku wanda ya yi sanadin rasa rayukansu a turmutsutsun bin layin karbar fom din a makon da ya gabata.

Shi dai wannan karbar fom na tallafin noma da kiwo na APPEALS da wannan al’amari ya faru, ya tara dubban mutane maza da mata daga garuruwa da kauyuka na Kananan Hukumomin Kubau, Kauru da Lere wanda ya kawo cunkushewar wajen.

Da yake yiwa wakilinmu karin bayani kan wannan al’amari, daya daga cikin wadanda suke bayar da tsaro a wajen kuma ma’ajiyin kungiyyar ‘yan sintiri na Karamar Hukumar Lere Malam Aliyu Yahaya, ya bayyana cewa yanayin cunkoson jama’a ne yasa aka sami wannan matsala, wanda ya kai ga rasa rayukan yara jirajirai guda uku, da wata mata da ta suma, amma daga baya ta farfado.

Ya ce wadanda suka rasu din, jarirai ne da ake goyansu a baya. Kuma sun rasu ne sakamakon layin da matan suka yi, suka matse wadannan yara har suka mutu.

‘’Mun yi ta cewa matan kowace mata ta kwance goyon ta, ta rike a hanu saboda gudun faruwar wannan al’amari, amma wasu matan suka ki jin maganarmu. Har aka kai ga matse wadannan yara suka mutu. Farko a shekaran jiya guda biyu suka rasu, washe gari kuma guda daya ya rasu. Sai wannan mata da ta suma sakamakon wannan cunkoso da zafi’’.

Ya ce wannan shiri na mata da maza ne, amma sai mata suka fi yawa a waje domin mata daga garuruwa da kauyuka daga ko’ina a kanannan hukumomin Kauru da Kubau da kuma nan Lere ne suka halarci wannan waje, domin karfar wannan fom na tallafin noma da kiwo.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin jami’an da suke gudanar da wannan shiri da aka turo kan wannan al’amari amma sunki yin magana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here