Yadda Gidauniyar Annur Ta ke Kyautata Rayuwar Al’umma

0
884
Wani aikin Samar da ruwa da Gidauniyar Annur ta gudanar a garin Kwa, cikin yankin karamar hukumar Dawakin Tofa.
JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

GIDAUNIYAR Annur wadda aka fi sani da “Annur Foundation Kibiya” tana kara cimma  nasarori masu tarin yawa idan aka dubi irin  aiyukan da take yi domin kara kyautata rayuwar al’umma tun kafuwarta kimanin shekaru hudu da suka gabata.

Sannan ana ganin irin  kyawawan aiyukan da gidauniyar take aiwatarwa kuma a garuruwa da unguwanni daban-daban ba tare da nuna gajiyawa ba, wanda  hakan ce  ta sanya  ake yi mata fatan alheri da kuma godiya kodayaushe.

Akwai jerin tambayoyi da mutane keyi kan aiyukan wannan gidauniya ta Annur, tare da neman karin bayani kan aiyukan ta da manufofin ta, inda  ba tare da bata lokaci ba jagoran gidauniyar, Dokta Aliyu Musa Aliyu Kibiya, yayi Karin bayani kan yadda wannan gidauniya take aiyukan ta da sauran abubuwa muhimmai da al’umma basu sani ba.

Wani aikin Samar da ruwa da Gidauniyar Annur ta gudanar a garin Kwa, cikin yankin karamar hukumar Dawakin Tofa.

Dangane da maganar ciyar wa cikin wannan wata na Ramadan, an yi tambaya kan yadda aikin ciyarwar ke gudana, inda  jagora Dokta Aliyu Kibiya ya ce sun gamsu da yadda shirin ciyarwar yake gudana a cibiyoyi sama da 30, kuma mutane masu tarin yawa suke buda baki cikin jin dadi da walwala a kullum.

Sannan yayi tsokaci dangane da yadda aikin bada ilimi da tarbiyya yake tafiya a makarantar koyar da marayu da sauran masu bukata dake garin Kibiya inda  yaran ke koyon karatu na alkur’ani da haddarsa bisa kwazo.

Bugu da kari, jagoran gidauniyar ta Annur Dokta Aliyu Musa Aliyu Kibiya ya bayyana cewa ana samun nasarar karatu a  wata makarantar Allo dake garin kura wadda aka zaba ana gwajin karatun Allo a zamanance domin bunkasa ilimin addini da magance yawaitar barace-barace da almajirai ke yi.

Haka kuma kamar yadda bayanai suka gabata a baya, gidauniyar Annur tana shirin kafa wata cibiyar kula da lafiyar al’umma a garin Dangwauro tare da samar da likitoci da masu duba lafiyar al’umma kwararru domin bada gudummawa ta fannin lafiya cikin yardar Allah.

A karshe, Dokta Aliyu Kibiya, jagoran gidauniyar Annur, ya bada tabbacin cewa gidauniyar zata ci  gaba da bullo da shirye-shirye na kyautata zamantàkewar jama’a a  aikace kamar yadda yake kunshe cikin manufofin kafata ba tare da nuna gajiyawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here