Buhari Ne Ya Zabi Gbajabiamila A Matsayin Kakakin Majalisa Ba Tinubu Ba – inji El-Rufa’i

0
541

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNAN jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai yayi karin haske akan maganar dake yawo a tsakanin jama’a cewa Bola Tinubu shi ne ke son Femi Gbajabiamila ya kasance kakakin majalisa ta 9, inda gwamnan yace shugaba Buhari ne ya zabe shi ba Tinubu ba.

El-Rufai yayi wannan jawabin ranar Juma’a yayin da tawagar kamfe ta Femi/Wase wacce ke kunshe da yan majalisa 120 ta kai masa ziyarar bangirma a fadar gwamnatin jihar Kaduna.

Gwamnan ya kara da cewa, an zabi Femi a matsayin wanda zai kasance kakakin majalisa ta 9 saboda kwarewarsa a siyasa, musamman idan aka yi duba zuwa bangaren majalisar dokoki.

“ Akwai wani rudani kan cewa Bola Tinubu shi ne ya fito da Femi a matsayin dan takarar kakakin majalisa. Amma gaskiyar lamarin shi ne shugaba Buhari ne da kan sa ya fito da shi a matsayin dan takarar saboda jajircewarsa da kwarewa a harkokin majalisar.

“ Wasu daga cikin takwarorinmu sun so kawo kace nace akan lamarin. Sai dai wannan abu sam bai yi tasiri ba saboda duk yadda mutum zai yi sai ya nemi wanda zai samu saukin aiki da shi. Shekara hudu da suka wuce mun dandana kudarmu a hannun majalisar dokoki, a nan Kaduna ni da kaina na zabi kakakin majalisa.

“ Jihar Kaduna ta aminta da maganar Buhari kuma ina tabbatar muku ranar 11 ga watan Yuni da za a kaddamar da sabbin shugabannin majalisa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here