Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranakun Hutun Karamar Sallah

0
527

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN tarayya ta kaddamar da Talata, 4 ga watan Mayu da Laraba, 5 ga watan Mayu a matsayin ranakun hutu domin bikin karamar sallar.

Sakatariyar din-din-din na ma’aikatar cikin gida, Barista Georgina Ekeoma Ehuriah ta sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya a ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu ta hannun Daraktan labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Mohammed Manga.

Ta taya Musulmai murnar kammala azumin Ramadana cikin nasara sannan ta bukaci dukkanin yan Najeriya da suyi amfani da bikin wajen addu’an zaman lafiya, hadin kai, ci gaba da daidaitar kasar.

Ta bukaci yan Najeriya da su guji kalamun kiyayya da hada hannu da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen Gina zaman lafiya, da hadin kai mai karfi a Najeriya domin cika cigaban da ke kunshe da mataki na gaba.

Barista Ehuriah ta sake ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya ya jajirce domin kare yan Najeriya, inda ta kara da cewa hukumomin tsaro, a karkashin ma’aikatar sun yi umurnin tabbatar da samar da ingantaccen tsaro a lokaci da bayan bikin Sallah.

Ta kuma jadadda cewa gwamnatin tarayya na fatan dukkanin yan Najeriya za su ci gaba akan koyarwar wata mai tsarki ta hanyar yin Sada ka, da soyayyar juna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here