Gwamnatin Zamfara Ta Taimakawa Al’ummar Nawaje Su Dawo Daga Gudun Hijira – Sarkin Yamman Akuzo

0
657

Isah Ahmed, Daga Jos.

HAKIMIN Sarkin Yamman Akuzo da ke karkashin kasar Wonaka ta gabas, a masarautar Gusau da ke Jihar Zamfara Alhaji Muhammadu Adam ya yi kira ga gwamnatin Jihar Zamfara, da ta taimakawa da al’ummar garin Nawaje da ke yankin Akuzo da jami’an tsaro, domin su dawo garin daga gudun hijirar da suka yi, zuwa wasu garuruwa a jihar.

Hakimin Sarkin Yamman Akuzo ya yi wannan kiran ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.

Hakimin ya bayyana cewa halin da garin Nawaje yake ciki yanzu ya fashe gabaki daya, babu kowa a cikin garin.

Ya ce “akwai gidaje sama da 1000 a garin kuma a kalla akwai mutane sama da dubu 10 a garin, amma yanzu duk an watse babu kowa don ‘yan ta’adda ne suka shigo garin suka tarwatsa garin kwanakin baya.

Ya kara da cewa mutanen garin tsofaffi da kananan yara maza da mata sun yi gudun hijira sun warwatsu zuwa garuruwan Mada da Kwatarkwashi da ‘Yan doto da kuma cikin garin Gusau don haka yanzu wannan gari ya zama kufai babu kowa a garin. don haka yake rokon gwamnati ta tallafawa al’ummar wannan gari da jami’an tsaro, domin su dawo garin musamman ganin mawuyacin halin da suke ki, sakamakon wannan gudun hijira da suka yi.

Ya ce “babu shakka idan gwamnati ta tallafawa al’ummar wannan gari suka dawo zasu zo su shiga aikin noma ganin ga damina ta fadi.”

Hakimin ya yabawa Mai martaba Sarkin Gusau Alhaji Ibrahim Bello da Uban kasar Wonaka ta gabas Mai girma Alhaji Muhammad Abdulkadir kan kokarin da suke yi, wajen ganin an warware matsalar tsaro da take damun al’ummominsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here