Yan Sanda Sun Tarwatsa Yan Shi’a Dake Zanga-Zanga A Kaduna

0
630

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

AN shiga halin dar-dar a rana Juma’a 31 ga watan Mayu a jihar Kaduna lokacin da jami’an yan sanda suka bude wutan harbi a sama domin tarwatsa mambobin kungiyar Shi’a, wadanda suka mamaye unguwanni domin zanga-zangar ci gaba da tsare shugabansu da gwamnati ke yi.

El-Zakzaky da uwargidarsa Hajiya Zeenat Ibrahim da wasu yan kungiyar na fuskantar tuhume-tuhume a babbar kotun jihar Kaduna da kotun Majistare bayan an kama su a watan Disamban 2015 biyo baya karawa da suka yi da sojoji a Zariya.

Dubban yan Shi’an, wadanda suka hada da mata da maza matasa, sun fara zanga-zangar jim kadan bayan sallar Juma’a a hanyar Kano inda suke ta ihun “Allahu Akbar, a saki shugabanmu”.

Yayinda suka mamaye hanyar Ahmadu Bello Way, babbar birnin Kaduna, sai kawai hukumomin tsaro suka tarwatsa su ta hanyar harba barkonon tsohuwa a sama, inda hakan ya tursasa masu zanga-zangar bin hanyoyi daban-daban.

Masu zanga-zangar sun haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da kuma wadanda suka yi sallar Juma’a a yankin, domin hakan ya tursasa mutane yin gudu domin tsira da tsoron fadawa cikin rikicin wanda Harbe-harben yan sanda ya kara haddasa tsoro a tsakanin mutane.

Yan sandan sun kakkabe hanyoyin Ahmadu Bello Way, Kano Road, Ibadan Street, Abeokuta Street da sauransu, yayinda suka daidaita cunkoson hanya domin mutane su samu damar zirga-zirga cikin sauki sakamakon cunkoson da aka samu.

Sai dai babu tabbacin ko yan sanda sun kama masu zanga-zangar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here