El-Rufa’i Ya Yi Sabbin Nade-Nade Guda Biyar

0
632

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNAN jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya sake nada Samuel Aruwan, a matsayin mai magana da yawunsa a karo na biyu.

Tun bayan bikin rantsuwa sabbin zababbun gwamnoni suka fara bayar da wasu daga mukaman siyasa a jihohinsu.

Aruwan, wanda tuni sunansa ya zama sananne a jihar Kaduna da kewaye, ya kasance kakakin gwamna El-Rufa’i a zangon mulkinsa na farko.

Labarin nadin Aruwan tare da ragowar mutanen, na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Salisu Suleiman, sakataren gwana El-Rufa’i, ya fitar da yammacin ranar Asabar.

Ga sunayen wadanda aka nada tare da Aruwan:
1 – Maryam Abubakar, Babban mai taimakawa wa gwamnan El-Rufai kan sabbin kafafen yada Labarai.
2 – Saude Amina Atoyebi, Babban mai taimakawa gwamnan a kan Ayyuka.
3. Mukhtar Maigamo​​, Mai taimakawa wa gwamna a bangaren hulda da jama’a
4. Manasseh Istifanu, Mai taimakawa gwamna a kan harkokin yada Labarai.
5. Nuhu John Gwamna, mai daukan hoto na musamman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here