Gobe Sallah, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Sanar

0
845

Daga Usman Nasidi.

LABARIN da muke samu kai tsaye daga fadar mai alfarma sarkin Musulmi, Sultan Abubaakar Sa’ad na nuna cewa an ga sabuwar jaririyar watar Shawwal, a yau Litinin 29 ga watan Ramadan wanda yayi daidai da 3 ga watan Yuni, 2019.

Sarkin Musulmi ya sanar da cewa gobe, ranar Talata ce daya ga watan Shawwal kuma ranar Sallar Eidul Fitr.

Yace: Bisa ga shari’ar Musulmi, muna masu sanar muku da cewa a yau Litinin 3 ga watan Yuni 2019 wanda yayi daidai da 29 ga watan Ramadan 1440, ne karshen watan Ramadana na shekarar 1440AH.”

“Mun samu rahotannin tabbacin ganin wata daga shugabannin adinin Musulunci daga gari daban-daban. Mai martaba Shehun Borno, Sarkin Gwandu, Sarkin Jema’a, Sarkin Damaturu, da wasu sa sassan jihar sokoto.

Bisa da haka, gobe Talata 4 ga watan Yuni, 2019 ta zama daya ga watan Shawwal 1440AH kuma ranar Sallah. Muna rokon Allah ya karba ibadun da mukayi a cikin watar Ramadan.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here