Daga Usman Nasidi.
DA Sanyin Safiyar jiya ne Sabon Gwamnan Jihar Zamfara Dakta Bello Mohammed Matawalle Maradun ya kai ziyarar gani da Ido a garin Lilo dake yankin Mada A Karamar Hukumar Gusau inda barayi suka Kora mutanen garin da sauran wasu garuruwa da ke kewaye da garin Mada.

Gwamnan ya nuna Bakin cikinsa da irin yadda matsananciyar rashin tsaron da al’ummar wannan garin suke ciki na zaman dar-dar.
Al’umma da dama ne suka fito domin tarbon Gwamnan tare da yi masa fatan alheri tare da addu’ar Allah masa jagoranci Ya kuma tsare shi.
Gwamnan dai yana tare da rakkiyar muhimman mutane daga cikin jahar Zamfara wadanda su ka hada Mataimakinsa da sakatarin gwamnati da Jami’an tsaro da dukkan masu yiwa Jihar Zamfara fatan alheri.
Ga hotunan ziyararsu a cikin gari da dajin
