Sheikh Gumi Ya Bukaci Buhari Ya Gaggauta Sakin Dasuki Da El-Zakzaky

0
896

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

FTACCEN malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta saki tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Sambo Dasuki ba tare da wani bata lokaci ba.

Kazalika, Malamin ya yi wani kira ga gwamnatin a kan ta saki shugaban mabiya kungiyar shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Sheikh Gumi ya yi wannan kira ne ranar Asabar yayin rufe karatun tafsirin watan azumin Ramadana a masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna inda ya ce akwai bukatar gwamnati take yi wa umarnin biyayya.

Gumi ya kara da cewa babu dalilin cigaba da tsare mutanen biyu tunda tuni kotu ta bayar da umarnin a sake su.

Ya ce zai fi sauki ga gwamnatin tarayya ta yi sulhu da Sheikh Zakzaky a kan cigaba da tsare shi a kurkuku.

“A nan gida Najeriya, ina son yin kira ga gwamnati da ta kara duba lamarin Kanal Sambo Dasuki domin a sako shi ba tare da bata lokaci ba, haka ma shugaban ‘yan Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

“Su sake shi idan ya so sai su tattauna da shi domin su fuskanci juna. Ba daidai bane gwamnatin ta ki yin biyayya ga umarnin kotu ba.

“Matukar gwamnati ba ta yi biyayya ga doka ba, dole a samu haramtattun kungiyoyi da zasu keta doka da gangan. Babu wani uzurin aikata ta’addanci.

“Dole gwamnati ta nuna kyakyawan misali ta hanyar sakin su, musamman kanal Sambo Dasuki ,” a cewar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here