Allah Ya Yiwa Tsohon Kwamishinan Kaduna, Abdulsalam Baba Ahmed Rasuwa

0
1262

Mustapha Imrana Abdullahi, Daga Kaduna.

ALLAH ya yiwa tsohon kwamishinan filaye na jihar Kaduna, Abdulsalam Baba Ahmed rasuwa, a ranar Talata, 4 ga watan Yuni bayan yayi fama da rashin lafiya.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 53 a duniya.

Babban dansa, Hakeem Baba Ahmed ne ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Zaria. Ya bayyana cewa mahaifin nasa ya rasu da misalin karfe 3:00 na rana a Kaduna.

Kafin a nada shi a matsayin kwamishina a gwamnatin Ramalan Yero, marigayin yayi aiki a matsayin shugaban karamar hukumar Zaria, sannan ya riki mukamai daban-daban a gwamnati na kungiyoyi masu zaman kansu.

Anyi sallar jana’izarsa a gidan ahlin Baba Ahmed da ke Tudun Wada, Zaria.

Kwanan nan ne dai iyalan Baba Ahmed suka rasa wasu daga cikin ahlinsu wadanda suka hada da Mahmoon, Mahadiyya da kuma Abdulrashid.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here