An Gurfanar Da Matar Da Ta Hada Kai Da Wasu Mutane Wajen Garkuwa Da Mijinta

0
760

Daga Usman Nasidi.

RUNDUNAR yan sanda a jihar Legas a ranar Litinin sun gurfanar da wata mata mai shekara 27, mai suna Elizabeth Sowemi, wacce ake zargin ta hada kai da wasu mutane uku domin su sace mijinta.

Sowemi ta gurfana a gaban kotun majistare da ke Ebute Meta kan tuhume-tuhume hudu.
Ana tuhumarta tare da Musibau Ayinde mai shekara 28, Kehinde Salisu mai shekara 45 da kika Jacob Ogunbiyi mai shekara 43.

Kotu bata saurari rokon wadanda ake tuhuma ba yayinda alkalin kotun Magistrate Adeola Adedayo tace tana bukatar shawara daga sashin DPP na jihar.

Ta tsare wadanda ake tuhuma a gidan yari zuwa lokacin da zata ji shawarar DPP sannan ta dage shari’an har zuwa ranar 6 ga watan Yuni domin ci gaba da zama.

Da farko, dan sanda mai kara, Sufeto Chinalu Uwadione, ya fada ma kotu cewa wadanda ake kara sun aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Mayu a Abule Egba da ke jihar Legas.

Dan sandan yayi zargin cewa Sowemi ta umurci Ayinde, Ogunbiyi da Salisu da su yi garkuwa da maigidanta, Moruf Sowemi mai shekara 53.

An tattaro cewa mazajen uku sun tsare mutumin a gidan Ogunbiyi a Oke Ola, Owode, Yewa, Idi Iroko, Ogun.

Uwadione ya fada ma kotu cewa wadanda ake kara sun bukaci naira miliyan biyar kudin fansa daga yan uwan Moruf domin sakinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here