Hukumar Yan Sanda Ta Yi Nasarar Damke Wani Dillalin Makamai

0
544

Daga Usman Nasidi.

HUKUMAR yan sanda Najeriya, ta yi nasarar kama wani dilan da ke sayarwa masu garkuwa da mutane makamai a karkashin aikin yan Operation Puff Adder.

Rundunar ta bayyana cewa bayan shigar sa hannun jami’an tsaro yayi iƙrarin cewa daga kasar Libiya da Burkina faso yake shigo da makaman.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ƴan sandan, ya gabatar da masu garkuwa da mutane su 38 da suka shiga hannu, ga yan jaridu gabanin kaisu kotu don sharia ta yi aikin ta.

Hakazalilka hukumar ta ƴan sanda ta kwace makamai masu yawa da suka hada da alburusai da bindigogi kirar AK47 masu yawan gaske a wajen Ƴan ta’addan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here