Gwamnatin Zamfara Ta Dakatar Da Sarkin Maru

0
810
Daga Mustapha Imrana Abdullahi.
Gwamnan Jihar Zamfara Dakta Bello Muhammad Matawallen Maradun ya Amince da batun dakatar da Sarkin Maru, Alhaji Abubakar Chika Ibrahim, da kuma Hakimin Kanoma, Alhaji Ahmad Lawan, nan take.
A cikin wata sanarwar da daraktan yada labaran Gwamnan ya sanya wa hannu Alhaji Yusuf Idris, kuma aka rabawa manema labarai, takardar ta ci gaba da cewa daukar matakin an yi shi ne sakamakon irin korafe korafen da aka samu a kansu na zargin da ake yi masu da hannu cikin ayyukan yan Bindiga da sauran laifuka.
Takardar ta ce sarkin tare da Hakimin za su ci gaba da zama a matsayin dakatattu har sai an Kammala binciken farko.
Tuni dai aka umarci sarkin da ya mika duk wadansu kayan Gwamnati da suke hannunsa ga babban Hakimin da ya fi kowa ne Hakimi girman mukami,yayin da shi kuma Hakimin Kanoma zai mika tasa ragamar ga mai unguwar da ya fi sauran girman mukamin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here