Majalisar Dokokin Kaduna Ta Yi Na’am Da Kudirin Yiwa Ayyukan Addini Iyaka

0
539

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

YAN sa’o’i kadan kafin a rufe majalisar dokokin jihar Kaduna ta takwas, majalisar ta rattaba hannu a kan kudirin yi wa ayyukan addini iyaka a jihar.

Idan ba a manta ba anyi ta yamutsa gashin baki game da shirin gwamnatin jihar karkashin jagorancin, Mallam Nasir El-Rufai na yi wa ayyukan addini iyaka a jihar.

Malaman addinin musulunci da na Kirista sun yi ta tofa albarkacin bakin su da yin Allah wadai da shirin yi wa ayyukan addini iyaka a jihar.

Kakakin majalisar jihar, Aminu Shagali ne ya jagoranci wannan zama.

Ita dai wannan doka idan gwamna ya sanya hannu zai yi wa ayyukan addini da ya hada da yin wa’azuzzuka iyaka.

1. Za a kirkiro da ma’aikata da zata rika tantance wa’azuzzuka da kuma malaman da za su rika yin wa’azi a fadin jihar.

2. Kowani malami sai ya mallaki lasisin yin wa’azi, musulmine ko Kirista.

3. Za a kafa irin wadannan ofisoshi a kananan hukumomin jihar wanda sune za su rika mika wa hukumar sunayen malamai da Fastocin da za a tantance sannan kuma aba su lasisin yin wa’azi.

4. Daga yanzu sai dai ka saurari wa’azin ka a cikin mota, gida, masallaci da da dakuna. Duk wanda aka kama ya kure wa’azi yana saurare zai dandana kudarsa.

5. Duk wanda ya kure karatu ko wa’azi ta lasifika daga karfe 11 na dare zuwa karfe 4 na safe zai yi kwanan gidan yariko kuma ya biya taran naira 200,000.

6. Daga karshe duk wanda aka samu yana fadin kalamun batanci ga wani ko addini zai biya taran naira 100,000 ko kuma a garzaya da shi kurkuku ko kuma duka.

Shi dai wannan kudiri, gwamnatin Kaduna ta mika shi majalisar jiha tun a 2016.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here