Gwamna Yahaya Bello Ne Zabin Mu – Kungiyoyin Dalibai

0
752
Daga Mustapha Imrana Abdullahi.

A Lokacin da zaben Gwamnan Jihar Kogi ke Kara gabatowa daliban manyan makarantun Jihar da na kasa baki daya sun bayyana aniyarsu na marawa Gwamna Yahaya Bello baya domin sake lashe zaben a karo na biyu.

Daliban dai sun yi kira ga daukacin al’ummar Jihar Kogi da kada su sake suyi kuskuren ba su dawo da Gwamna Yahaya Bello ba a zaben ranar 16 ga watan Nuwamba, sun kuma shawarci jam’iyyar APC da ta tabbatar da ganin an yi gangamin zabe kamar yadda ya dace domin samun nasarar ta tare da yayanta baki daya.

Shugabannin Kungiyar daliban sun bayyana hakan ne a wajen taron manema labarai na hadin gwiwa da suka yi a kwanannan a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kogi da ke Lokoja.

Kungiyoyin daliban sun hada da reshen jiha na Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) da Kungiyar daliban yan asalin Jihar Kogi (NAKOSS), Kungiyar dalibai ta al’ummar Igala (ISA),Kungiyar dalibai ta Ebira (NAES) da Kungiyar dalibai ta Okun (NAOS) da sauran su.

Da yake jawabi a madadin daliban kwamared Hussein Attaja, shaidawa manema Labaran ya yi cewa sun cimma wannan matsayar ne a wajen babban taron kungiyoyin na kasa inda Suka tattauna kuma Suka dauki matakin marawa Gwamnan da ke da amfani baya da ya San mutunci da darajar dalibai da kum sauran jama’ar Jihar baki daya.

Ya ci gaba da cewa “Gwamna Bello ne ya kasance zabinsu da zabin da ya ragewa kowa a cikin Jihar. Da ya nuna kauna ga dalibai ta hanyar tallafa masu a koda yaushe tare da matasa don haka a ranar sha shida ga watan Nuwamba sai Gwamna Yahaya Bello kawai za a zaba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here