Uwargidan Marigayi Tsohon Gwamnan Taraba Ta Amarce Da Wani Matashi

1
1087
Daga Mustapha Imrana Abdullahi.
UWARGIDAN marigayi tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai, ta samu nasarar auren wani matashin Dan kasuwa kuma shugaban kamfanin ITBAN, Haliru Sa’ad Malami, da Ake yi wa lakabi da Turakin Malumfashi.
Emmanuel Bello, Mai taimakawa tsohon Gwamnan ya bayyana cewa Amaryar dama can cikin musulunci take duk tsawon rayuwarta.
Wata majiya ta bàyyana cewa Malami, Matashi ne wanda ke cikin shekarunsa na Talatin, kuma Dan uwa ne ga matar marigayi tsohon shugaban kasa Turai Yar’aduwa.
Ita dai Hauwa tare da mijinta Danbaba Suntai tsohon mijinta ya samu hadarin jirgin sama ne da ya rutsa da Shi a watan Okutoba 2012 ya kuma mutu a watan ranar 28, ga watan Yuni  2017 a Houston, da ke Florida ta kasar Amurka.
Malami ya auri Hauwa wadda take cikin shekarunta na Hamsin a wani Dan Kwarya kwaryan taro a babban masallacin Abuja ranar Asabar.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here