Allah Ya Yiwa Sanata Babayo Gamawa Rasuwa

0
652

Daga Usman Nasidi.

TSOHON mataimakin shugaban jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) na kasa, Sanata Babayo Gamawa ya rasu.

Ya rasu ne na yau Juma’a 14 ga watan Yuni a garin Bauchi bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Isah Garba Gadau, mai magana da yawun sa ya tabbatar da rasuwarsa.

“Ya yi koka cewa cikin sa na ciwo kuma aka tafi da shi asibitin koyarta ta Jami;ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) inda aka ba shi gado. Yanzu haka ina hanyar zuwa gidan sa,” inji mai magana da yawun sa.

Kafin rasuwarsa, Sanata Gamawa ya taba rike mukamin mataimakin gwamnan jihar Bauchi a jam’iyyar APC kafin zaben 2019 bayan jam’iyyar PDP ta dakatar da shi.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 53 a duniya.

Tsohon dan siyasan ya taba zama kakakin majalisar jihar Bauchi a lokacin mulkin tsohon gwamna Isa Yuguda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here