An Bukaci Yan Majalisu Da Al’umma Su Taimakawa Nakasassu

  0
  629

  Musa Muhammad kutama, Daga kalaba.

  AN bukaci yan majalisun tarayya da masu hannu da shuni dake arewacin Najeriya dama kasa baki daya da su rika daukar nauyin kananan kungiyoyin wasannin motsa jiki musamman na nakasassu ganin cewa sun mayar da hankalin su wajen yin wasanni ba dogara da yin barace-barace ba.

  Nakasassun rungumi wasannin motsa jikin ne matsayin wata hanya ta sana’a da kuma neman abinci.

  A ranar talata da ta gabata ne aka yi wasan sada zumunci tsakanin qungiyar wasan kwallon kafa ta guragu dake Uyo jihar Akwa Ibom da takwararta ta Kalaba jihar kuros riba.

  Wani dan kasuwa Alhaji Mukhtari Abubakar Manga dake kalaba ne ya bukaci hakan lokacin da ya zanta da wakilin mu jim kadan da kaddamar da wasan motsa jiki na kwallon guragu da akafi sani da suna parasoccer a filin wasa dake layin mary slessor kalaba jihar kuros riba.

  Guragu mazauna jihohin Akwa Ibom da kuros riba ne suka shirya wasan sada
  zumunta tsakanin su na kungiyoyin biyu.

  Dan kasuwar ya ci gaba da cewa “ Ina kira ga ‘yan majallisun tarayya dana jihohi dama masu hannu da shuni da su rika daukar dawainiyar kungiyoyin wasannin motsa jiki na masu larurar nakasa musamman ‘yan arewa nakasassu mazauna kudanci tunda yawancin guragunnan suna da iyalan da suka baro su a gida kuma sune suke daukar dawainiyar iyalan su wanda ya hada da biyan kudaden makarantar ‘ya’yan su sannan zaman da suke yi anan kudu haya suke biya.”

  Manga ya kara da cewa rayuwa a kurmi tana da tsada donyawanci abubuwan anan suna da tsada kana wasu lokutan suna shan magani na kula da lafiyar jikin su don haka yake rokon ‘yan uwan da su rija taimakawa suna zuwa dubasu lokaci zuwa lokaci don ganin irin ta yadda za’a taimaka musu.

  Dan kasuwar, ya kara jadda bukatar da ke akwai na a rika tallafawa ‘yan wasan saboda halin da suke ciki koda tsufa yazo musu ‘ya’yan su da suka baiwa ilmi zasu taso su rika taimaka musu.

  Tun farko a hira da wakilin mu shugaban jungiyar wanda shi ne kyaftin din kungiyar SAS, Gambo ya ce makasudun shirya wannan wasan sada zumunta shi ne domin sunyi azumi sun gama lafiya sai sukace to bari mu hada wani wasa tsakanin su da makwabtan su saboda su kara dankon
  zumunci tsakanin su don murnar biki sallah.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here