An Ci Kulob Din Kano Filas Tarar Naira Miliyan 8

  0
  971

  Daga Mustapha Imrana Abdullahi.

  HUKUMAR shirya wasannin Firimiya Ta kasa a tarayyar Najeriya ta bayyana dakatar da kaftin din Kano filas wato Rabi’u Ali Fele, Hana shi yin wasanni sha biyu da kuma cin Kulab din tarar naira Miliyan Takwas da kuma yanke wa Kulab din yin wasa uku ba tare da yan kallo ba.

  Shi dai laifin da aka ce yasa aka yanke wa kaftin din wannan hukunci na Hana Shi yin wasanni sha biyu shi ne jagorantar wadansu yan kallo da suka shiga fili tare da lalata shingen da aka sa tsakanin filin da yan kallo da suke a bayan fage.

  An dai ce lamarin ya faru ne sakamakon irin yadda aka tashi wasan da Kulab din Kano filas ya yi da Kulab din Enugu Rangers da aka tashi Wasan kowa na da ci daya, wannan ne yasa yan wasan suka fusata.

  Rahotanni dai sun bayyana cewa magoya bayan wannan kula na Kano filas ba su ji dadin lamarin ba inda suke fatar a rage wannan hukunci saboda sun bayyana shi da cewa ya yi masu tsauri kwarai.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here