Yadda Wasu Tagwaye Suka Yi Mutuwar Ban Mamaki a Garin Jos

0
912

Isah  Ahmed, Daga Jos.

WASU tagwaye ‘yan biyu Isah Muhammad da Dauda Muhammad ‘yan shekaru 22 da haihuwa, da suke zaune a garin Jos babban birnin Jihar Filato, sun yi rasuwar da ta baiwa kowa mamaki a daren ranar litinin  da ta gabata.

Su dai wadannan tagwaye ‘yan biyu da suke zaune a unguwar Rikkos da ke garin na Jos, sun rasu ne a daidai ranar da aka haifesu da daidai yadda aka haifesu da kuma daidai lokacin da aka haifesu, ba tare da wata doguwar jinya ba.

Da yake yiwa wakilinmu karin bayani yayan wadannan tagwaye ‘yan biyu, Alhaji Musa Yaro Rikkos ya bayyana cewa wannan rasuwa ta wadannan tagwaye ‘yan biyu, tazo da abin al’ajabi, domin kusan yadda Allah ya kawo su duniya haka Allah ya karbi abinsa.

Ya ce  lokacin da aka haifi wadannan tagwaye ‘yan biyu shekaru 22 da suka gabata, an fara haihuwar Muhammad Isah ne a gida, sai haihuwar tayi tsanani,  sai aka nemo mota aka dauki mahaifiyar tasu zuwa asibiti, toh kafin a karasa zuwa a asibitin, sai aka haifi na biyun Muhammad Dauda kan hanyar zuwa asibitin.

Ya kara da cewa da Allah ya tashi karbarsu dayan da aka fara Haifa Muhammad Isah, babu wani dogon rashin lafiya a ranar litinin din sai, jikinsa ya canza sai aka  kira likiti don ya kara masa ruwa a gida.

Ya ce “an fara kara masa ruwan ke nan, ba a dade ba sai Allah ya karbi abinsa, ya rasu da misalin karfe 8:30 na dare.”

‘’Da na fito na sami daya dan biyun Muhammad Dauda a waje tare da abokansa sai nace masu ya kamata mutuwa ta zamo darasi a gareku. Ana gaya maku kuna kin yarda saboda kuruciya, ga wane Allah ya yi masa rasuwa. Sai na tafi gida naje na kwanta. daya dan biyun Muhammad Dauda yana nan har karfe 10:30  na dare a waje, sai ya ce bari yaje ya kwanta. Ya shiga daki ya kwanta ya yaja bargo ba a dade ba, sai wadanda suke kwana tare da shi suka ji ninfashinsa ya fara sama sama, sai suka je suka taso ni. Nazo na dauko mota a guje na dauke shi zuwa a asibiti da misalin karfe 11:00 na dare kafin na karasa asibitin Allah ya yi masa rasuwa, muka shiga asibitin likita ya tabbatar da rasuwarsa’’.

Acewarsa, abin mamaki wadannan tagwaye an haifesu ne a ranar litinin shekaru 22 da suka gabata, kuma suka rasu a ranar litinin daidai lokacin da aka haifesu, kuma wanda aka fara haifa a gida ya rasu a gida, dayan kuma da aka haifa a hanyar asibiti shi ma ya rasu a kan hanyar zuwa asibiti.

Alhaji Musa Rikkos a bayyana cewa babu abin da zasu ce kan wannan al’amari, domin sun san kowanne mai rai mamaci ne,  idan lokaci ya yi. Don haka sai ya yi addu’ar Allah ya jikansu ya gafar ta masu kurarensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here