Kaicho Matasa! Ina Muka Baro Tarbiyarmu Da Al’adu

  0
  737

  Daga Engr. Comrd Usman Nasidi.

  ALALHAKIKA, tarbiya wata abu ce wacce take nuni da irin halayya da dabi’u na yan Adam, kana tana nuni akan yanayin gudanar da rayuwar al’umma, wanda ya kunci addinin mutune, jinsinsu da al’adarsu, amma yanzu a wannan zamanin wasu matasa sun maye gurbin halayyarsu da sana’ar Shaye-Shaye da Karuwanci.

  Wato a zamanin yanzu, tarbiyar wasu mutanen ta zamanto wani abun Allah Wadai dubi da irin dabi’u ta yadda wasu matasan suka tsinci kansu a yayinda suka watsar da tarbiyar da aka sansu da ita, musamman Yaran Hausawa kuma matasa yan shekaru ashirin da dori har izuwa talatin da biyar ko kuma kasa da shekaru ashirin na wannan zamanin.

  Yara matasa maza da mata a yanzu sun dauki wani sabon salon rayuwa wacce suke ganin ita ce hanya mafi dacewa domin baya ga shaye-shayen, ashararanci da karuwancin da suka sanya kansu a ciki ba dare ba rana, babu wata sana’a ko aikin da suke yi wanda ya wuce wadannan, dukda yake mafi akasarin wuraren ashararanci da ake gudanar da ire-iren wadannan al’amuran ada, su kan kasance korarrun mutane ne ke zuwa suna yi ko wadanda suka gudu suka bar gidajensu, to amma a yanzu matasan da suka sunci kansu a cikin irin wannan halin, suna yi ne ta hanyar taimakon iyayensu domin iyayen nasu basa lura da harkoki ko al’amuran su ta yadda ya kamata baya ga goyon bayan da suke basu ta hanyar sakacin da suke yi.

  A halin yanzu, matasan yaran maza da mata sun koma cikakkun yan kwaya da shaye-shayen duk wasu kayan maye akowani lokuta, kana wasu daga cikin yaran mata sun zama cikakkun karuwai ayayinda suke aikin karuwanci a mafi akasarin wuraren ashararanci dake ciki da wajen garuruwan da suke, koda yake wasu daga cikin yaran na amfani da damar iyayensu basa lura da harkokinsu ne ko kuwa suna amfani da damar ba a gaban iyayensu suke ba don tayu kila makaranta aka tura su kuma iyayen basa damuwa da zuwa ziyartarsu don sanin irin halin da suke ciki, wanda ganin hakan ya basu damar sheke ayarsu ba makawa.

  Bincike ya tabbatar da cewar mafi akasarin daren ranakun Juma’a, asabar da lahadi kamar yadda wakilinmu ya ganewa Idonsa a wani kewayen gani da Ido daya kai, ya ganewa Idonsa irin ta’ammali da ta’annatin dake gudana a wasu wajejen shakatarwan, inda ya yi kukan wayyo Allah Kaicho na, dubi da ganin irin yanayin mummunar halin da al’ummarmu na wannan zamanin suka shiga musamman yaran Hausawa kuma Matasa wanda akasarinsu dake cikin wannan yanayi sun watsar da duk wata tarbiyar da suka samu, ko suke da ita face harkar shaye-shayen da karuwanci da suka sanya a gaba kawai.

  To amma abun tambaya anan shi ne shin wai iyayensu suna sane da irin halin da yaransu suke ciki ko kuwa yaran sunfi karfin iyayensu nasu ne, kana gwamnati da hukumomin jami’an tsoro na sane da irin wadannan al’amuran, don kuwa wasu yaran daga gidajen iyayensu suke fitowa domin zuwa wajajen sharholiyarsu ayayinda wasu kuma kama dakuna suke yi ko zaman dirshan a dakunan otel din wajajen ta hanyar tarewa da zama a gidajen baki daya.

  Wato a zamanin ada, tarbiya ta kasance wata ginshiki dake dora mutane akan duk wata turba wacce ke koyi da koyarwa irin wacce mutane kamilallu suke bayyanawa kuma ta kasance wata babbar abun alfahari dubi da yadda ake tafiyar da ita ada. Babu shakka, iyaye ada kan jajirce matuka wajen ganin yaransu sun samu wannan tarbiyar ta hanyar da duk ya dace, ya-Allah ko akan ‘ya mace ce ko ‘da namiji kuma babu shakka Jama’a na kokarin ganin an wanzar da wannan tarbiyar a wannan lokacin kuma jama’ar na kokarin yin koyi da hakan.

  Hakika idan akayi la’akari da irin halayya da dabi’u na mutanen da, za a iya tabbata cewa tarbiyar ada tana da tasiri matuka ta yadda babu wata hanyar da wani zai iya kushe ta, face saidai ya yaba da abinda ke gudana dubi da irin yanayin salon gaisuwa na mutanen, natsuwa, zamantakewa da yanayin huldarsu da sauran Jama’u yayinda duk suka hadu.

  To amma abun tambaya anan shi ne, shin a wannan zamanin yanzu, ita tarbiyar nan tana da tasiri har izuwa yanzu ko kuwa tana aiki ga yan bana bakwai, kuma shin kuma ko iyaye na kokari wajen ganin sun rama aikin alherin da suka samu a wajen iyayensu izuwa ga nasu ‘ya’yan ko kuwa sun watsar da ita ne domin jindadin duniya da biyewa sha’anin rayuwar duniya?

  Babu shakka, idan mukayi la’akari da irin tarbiyar mutanen da, dana mutanen yanzu musamman matasa, za a iya banbance tsakanin aya daga tsakuwa domin basu da alaka da juna ta yadda za a iya misiltasu ta kowani bangare ko fanni.

  Alalhakika, iyaye ya kamata su fargo daga dogon barcin da suke yi kamin suyi nadamar kuskuren sakacin da suke yi domin mafi akasarin yaran dake fita zuwa wajajen sharholiyar ashararancin, iyayensu na zaune dasu ne a gidajensu ayayinda abokansu ko kawaye ke amfani da damar sakacin su wajen kiransu domin su fito zuwa wajajen shakatawar su.

  Haka kuma, ya kamata bayan iyaye sunyi bankwana na sai da safe da yaransu, ai rika komawa su bincika ko yaran nan na kwance a dakunan su domin mafi akasarin yaran na amfani da damar idan iyayen sun shiga wajen barci, sai su kama hanyar zuwa wajen bidirin su, ayayinda wasu yaran kuma na amfani da wata damar ne da sunan zuwa ziyara wajen wasu abakonsu ko kawaye, kuma da wata shiga ta daban, sannan bayan sun fito daga gidajensu sai su canza hanya kana su canza shigar da suka yi domin wucewa wajen sharholiyarsu kamin daga karshe su dawo gidajen iyayen nasu su kwana.

  A karshe, muna masu kara jan hankalin iyaye da hukumomin dake da alhakin kula da lura da irin wadannan al’amuran akan su kara jajircewa wajen ganin an samu gagarumar nasarar magance wannan matsalar ko annobar data kunno kai tun kamin lamuran su zarce inda ba a zato, domin kuwa kowani dan adam da Ubangiji ya sanya wani a karkashin shi ko ya bashi arziki na ‘ya’ya, to babu shakka kiwo ce aka basu wanda dole za suyi bayanan yadda suka gudanar da kiwon nasu.

  Ubangiji Allah Ya kara shiryar damu da duk wata zuri’a baki daya, kana ya kowa mana mafita ga wannan mummunar al’amarin na gurbacewar tarbiya cikin sauki, tun kamin mu kaiga yin ayyukan danasani wacce bata da alfanu ga rayuwarmu ko na ‘ya’yanmu.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here