Hukumar NDLEA Tana Kara Samun Nasara A Kano – inji Kwamandan Jihar

0
677
JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

KWAMANDAN hukumar hana sha da  fataucin miyagun kwayoyi na jihar kano, Dokta Ibrahim Abdul yace ana samun ci gaba wajen yaki da shan miyagun kwayoyi da sauran kayan maye  a fadin  jihar,  bisa  la’akari da  kokarin  da hukumar keyi  bisa  taimakawar gwamnatin kano da kungiyoyi masu rajin hana shan miyagun kwayoyi.


Wasu daga cikin kayayyakin maye da hukumar NDLEA ta kama a Kano.

Kwamandan ya yi wannan bayani ne a hirar da suka yi da wakilinmu a hedikwatar hukumar jim kadan bayan kammala taro  da manema labarai inda ya sanar  da cewa ko shakka babu shan miyagun kwayoyi ya ragu sosai a jihar kano, musamman ganin cewa kafin zuwan sa kano, an shelanta jihar a matsayin jihar da tayi fice  wajen shaye-shaye, amma yanzu ta koma  matsayi na uku cikin jihohi dake  da matsalar shan miyagun kwayoyi.

Ya ce  sun sami nasarar kame  kayan maye  da  awon su yakai Kilo 6,726,012 a gurare daban-daban, sannan sun Kama mutane 725 inda kuma 620 maza ne  yayin da aka Kama Mata 105 da ake  tuhuma bisa  laifuka daban-daban domin  yi masu hukumce-hukunce daidai da  laifikan su.

Dokta Abdul ya kuma shaidawa Gaakiya Tafi Kwabo cewa gwamnatin jihar kano bisa  jagorancin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje tana bada  dukkanin taimakon da  ake  bukata wajen  samun nasarar yaki da  miyagun kwayoyi, sannan ya ce suma  kafafen yada labarai suna bada gagarumar gudummawa wajen wayar da  kan al’umma kan illolin shaye-shaye da  sauran bayanai kan gyaran halayya.

Bugu da  Kari, Kwamanda  Dokta Ibrahim Abdul yace  sun sami nasarar kame wata gona  da aka shuka tabar Wiwi a yankin karamar hukumar Kumbotso tare da lalata dukkanin abin da  aka shuka wanda  hakan babbar nasara ce ga hukumar, inda kuma ya jaddada cewa zasu ci gaba da aikin kawar da shaye-shaye a jihar kano, tare da damke dukkanin wadanda suke da hannu wajen shigar  da kayan maye cikin al’umma.

Dokta Ibrahim Abdul ya bayyana cewa akwai matsaloli da suke dan  dabaibaye aiyukan hukumar wadanda suka hada da karancin ma’aikata da  rashim isassun kudaden gudanar da aiki da kuma rashin samun cikakken hadin Kai daga wasu al’ummomi, inda daga karshe ya yi alwashin cewa jihar  kano zata zamo abar misali cikin sauran jihohin wannan kasa ta fuskar raguwar shan miyagun kwayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here