Lai Muhammed Ya Ki Bayyana Gaban Kotu AKan Zargin Naira Biliyan 2.5

0
617

Daga Usman Nasidi.

TSOHON minstan labarai Lai Mohammed a ranar Laraba, ya ki bayyana a gaban Mai shari’ah Folashade Ogunbanjo Giwa na babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abuja, don ya yi bayani akan kudi Naira biliyan 2.5 da aka baiwa kamfanin Pinnacle Communication.

A zaman na ranar Laraba, an cigaba da sauraren karar da ake yima babban darakta na watsa labarai, Ishaq Kawu Modibbo, da kamfanin Pinnacle Communication da wasu mutum biyu.

Tsohon ministan na labarai, na cikin sunayen da mai gabatar da kara, Henry Emore ya bayar a matsayin shaidun hukumar hana ta’annaci da kudin kasa (ICPC) kuma ana tsammani zai bayyana gaban kotu don ya bayar da shaida a matsayinsa na tsohon minista da ya bayar da umurnin a biya 2.5 ga kamfanin Pinnacle.

Amma, bayan da ya kira shaidu biyu, mai gabatar da karan ya gaya ma kotu cewa ya so ya kira shaidarshi na gaba, tsohon ministan labarai amma bai samu halartar zaman kotun ba.

Emore ya bayyana ma kotun cewa Lai Mohammed yayi tafiya zuwa kasar waje amma ana tsammanin zai dawo Najeriya kafin ranar 31 ga watan Yuli.

Haka zalika ya bayyana ma kotu cewa Lai Mohammed ya bayar da shaidarshi a rubuce ga ICPC, a matsayinshi na tsohon minista.

Mai gabatar da karar ya kuma bayyana ma kotu cewa sauran shaidun da ya so ya kira sunyi tafiya zuwa kasar Saudiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here