An Bukacin Gwamnatin Buhari Ta Gyara Hanyar Jos Zuwa Kaduna

  0
  801

  Isah Ahmed, Daga Jos.

  WANI dan kasuwa da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, Alhaji Hamisu Rabi’u  Mai Manja Saminaka ya yi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan ta yiwa Allah ta gyara hanyar da ta taso daga Jos zuwa Kaduna domin ceto al’ummomin da suke bin wannan hanya, daga mawuyacin halin da suke ciki, sakamakon lalacewar da  hanyar tayi. Alhaji Hamisu Rabi’u Mai Manja ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

  Alhaji Hamisu, ya bayyana cewa gaskiya mutane suna matukar shan wahala a wannan hanya,  sakamakon lalacewar da  tayi shekara da shekaru,  musamman lokacin damina.

  Alhaji Hamisu Mai Manja  ya yi bayanin cewa  wuraren da wannan hanya tafi mugun lalacewa, sun hada  daga garin Saminaka zuwa Jos da  daga garin Pambeguwa zuwa  Saminaka da  kuma daga Gadar Gayan zuwa garin Panbeguwa.

  Ya kara da cewa wannan hanyar ta kai shekaru sama da 20 da lalacewa, domin tun lokacin gwamnatin Obasanjo aka ce an bayar da aikin wannan hanya suka ji shuru.

  Ya ce “gwamnatin Goodluck tazo ita ma aka ce an bayar da aikin wannan hanya, nan ma suka ji shuru. A rubuce an  ce an yi aikin gyaran wannan hanya.”

  Acewarsa, gaskiya idan gwamnati bata yi kokari tazo ta gyara wannan hanya ba, mutanen da suke bin wannan hanya,  zasu dada shiga cikin wani mawuyacin hali.

  ‘’Wannan hanya tana bada gagarumar gudunmawa wajen tattalin arzikin kasar nan. Domin  ta hada jihohin Borno, Gombe, Adamawa, Bauchi da Filato. Kuma  mutanen da suke bin wannan hanya, suna dauko kayayyakin amfanin gona kamar  wake da masara da shanu da taki, da sauran kayayyakin harkokin kasuwanci’’ – inji shi.

  Ya kara da cewa suna murna cewa wannan gwamnati ta su ce,  domin sun zabi shugaban kasa Buhari dari bisa dari  amma sun yi shekaru 4 ba a gyara  wannan hanya ba.

  Don haka yana rokon gwamnatin Buhari da dukkan sauran masu hanu kan wannan al’amari, su kawo  dauki kan gyaran wannan hanya, domin a cetu jama’ar da suke bin wannan hanya, daga mawuyacin halin da suke ciki.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here