Allah Ya Tseratar Da Magajin Garin Daura Bayan Shafe Wata 2 A Hannun Barayi

0
1136

Daga Usman Nasidi.

ALLAH Ya kubutar da magajin garin Daura, kuma surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Musa Umar Uba daga hannnun miyagun da suka yi garkuwa dashi tun kimanin watanni 2 da suka gabata.

Magajin garin Daura tare Abba Kyari bayan kubuto shi daga hannun masu garkuwa da mutane a gidan da yake ajiye

Rahotanni daga garin Daura sun tabbatar da haka, inda suka bayyana cewa a ranar Talata, 2 ga watan Yuli ne Magajin Gari ya dawo gida, cikin koshin lafiya, bayan jajirtattun jami’an Yan sanda sun kwatoshi.

Idan za’a tuna a ranar 1 ga watan Mayu ne wasu gungun yan bindiga guda hudu suka kai farmaki gidan Magajin garim Daura, inda suka yi awon gaba dashi yayin da yake zaune a kofar gidansa bayan sallar Magariba.

Bayanai sun bayyana akan yadda Yan sanda na musamman na IRT dake karbar oda daga babban sufetan Yan sandan Najeriya a karkashin jagorancin DCP Abba Kyari suka gudanar da aikin ceton Magajin Gari.

Abba Kyari da tawagarsa sun kaddamar da samame ne a gidan da yan bindigan ke rike da Magajin gari dake Samegu akan hanyar zuwa Madobi a cikin jahar Kano, anan aka dinga musayar wuta tsakanin Yan sandan da miyagun.

Basaraken ya isa birnin tarayyar ne a cikin wani jirgi mai tashi da saukar ungulu da misalign karfe 1:30 a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja.

Daga cikin wadanda suka tarbi basaraken sun hada da dogarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Kanal Muhammed Lawal Abubakar, wanda ya kasance surukinsa.

Sanye da farin kaya, an gano basaraken tare da wasu yaransa da wani mataimakin kwamishinan yan sanda, Abba Kyari.

Sai dai kuma, babu tabbacin ko an kais hi fadar Shugaban kasa, Abuja ko kuma wani gida mai zaman kansa.

Sai dai da yake Yan sandan sun fi su kwarewa da sanin makaman aiki, da wuta yayi wuta sai miyagun suka ranta ana kare, da haka ne Yan sandan suka ceto Magajin gari, suka mikashi zuwa gidan dake garin Daura bayan ya huta.

Yan uwa da abokan arzikin sun yi ta kwarara zuwa gidan don yin ido hudu dashi, kuma anyi sa’a ya isa gida cikin koshin lafiya, daga cikin wadanda suka fara isa gidan akwai Aminu Jamo, wani hamshakin dan kasuwa dan asalin garin Daura.

Shi dai magajin gari ya kasance kani ne ga mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, kuma tsohon kwanturola ne a hukumar hana fasa kauri ta kasa watau kwastam, haka zalika yana auren Hajiya Bilki, diyar babbar yayar shugaba Buhari, Hajiya Rakiya.

Bugu da kari, babban dogarin shugaban kasa Buhari, Kanal Muhammad Abubakar yana auren diyarsa Fatima

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here