Karamar Hukumar Lere Ta Gudanar Da Ayyukan Raya Kasa Guda 108

0
653

Isah  Ahmed, Daga Jos.

KARAMAR Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna ta sami nasarar gudanar da ayyukan raya kasa guda 108, a cikin shekara daya.

Shugaban karamar hukumar Alhaji Abubakar Buba ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro da ya yi da shugabanni da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar, don bayyana masu irin ayyukan da ya yi a shekara daya da hawa mulkin karamar hukumar.

Ya bayyana cewa sun sami nasarori da dama a shekara daya da suka yi suna shugabancin karamar hukumar inda suka yi ayyukan raya kasa  da dama a lunguna da sakonan  karamar hukuma da suka kai guda 108.

Ya kara da cewa a  bangaren ilmi sun  gyara makarantun firamare sama da guda 20 tare da  sanya masu kujeru da kayayyakin koyarwa.

Har’ila yau ya ce  a bangaren samar da  ruwan sha  sun haka fanfaunan tuka tuka guda guda 48 a garuruwa daban na karamar hukumar.

Acewarsa, sun gyara hanyoyin   a garuruwan Ramin kura da Jama’ar Iya da Hanyar Saminaka zuwa Saminaka Resort kuma sun yi kwalbatoci da hanyoyin ruwa a garuruwa daban daban na  karamar hukumar.

Ya ci gaba da crew’s sun tallafawa mata masu kananan sana’o’i guda 500 tare da tura matasa guda guda 62 don su koyo sana’o’i daban daban a karamar hukumar.

Ya ce  ‘’Akwai sauran ayyukan da bamu riga mun kammala ba kuma ya zuwa yanzu mun yi kashi 50 bisa 100 na ayyukan da muka ce zamu yi, a kasafin kudinmu na shekara ta 2019, kuma in Allah ya yarda nan da karshen wannan shekara zamu kammala sauran ayyukan da suka rage’’.

Alhaji Abubakar Buba ya yi bayanin cewa gwamnatinsu a bayyane take don haka basa tsoron duk wanda zai kalubalancesu, domin dukkan ayyukan da suka yi suna nan a kasa kuma a bayyane.

A karshe, ya yi kira ga al’ummar karamar hukumar da su hada kai don a ciyar da  karamar hukumar da al’ummar gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here