Zan Yi Kokarin Ganin Na Samarwa Matasan Ayyukan Yi – Jarman Wunti

  0
  783

  Isah Ahmed, Daga Jos.

  DAN takarar kujerar shugabancin Karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi karkashin jam’iyyar PDP kuma Jarman Wunti, Alhaji Sale Abubakar Sale ya bayyana cewa idan Allah yasa ya sami nasara, zai yi iyakar kokarinsa wajen ganin ya samarwa dibbin matasan Karamar Hukumar Toro ayyukan yi. Alhaji Sale Abubakar Sale ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

  Sale Wunti ya bayyana cewar kowa ya sani babbar matsalar da take damun al’ummar Karamar Hukumar Toro, shi ne rashin ayyukan yi ga matasa.

  Acewarsa, akalla akwai matasa  da suka kammala manyan makarantu sama da  170,  da basu da ayyukan yi a karamar hukumar. Haka kuma akwai ‘yan makaranta da dama da suke son su cigaba da karatu da kuma matasan da suke sana’a, amma da basu da jari.

  Ya ce ‘’Zamu yi iyakar kokarinmu wajen ganin wadannan matasa  sun sami abubuwan da zasu yi musamman ta bangaren noma, domin muna da  kasar  noma mai albarka  a wannan karamar hukuma kuma  mun shahara wajen  noman dawa da masara da waken soya.  A duk Najeriya an san sunan  wannan karamar hukuma, wajen noman dankalin hausa. Don haka zamu inganta wannan noma, ta yadda matasanmu zasu sami abin da zasu dogara da kansu’’.

  Ya kara da cewa  ta bangaren ma’adanai a duk jihar Bauchi babu wajen da ya kai karamar hukumar Toro yawan ma’adanai, domin akwai man fetur da gwal da kuza da za ayi amfani da su wajen inganta rayuwar al’ummar wannan karamar hukuma da Najeriya baki daya. Don haka ya bada tabbacin cewa idan Allah yasa ya sami nasara, zai tsaya wajen ganin al’ummar karamar hukumar sun ci gajiyar wannan arziki da Allah ya basu.

  Alhaji Sale Wunti, ya yi kira ga kananan hukumomin Najeriya  su daina tsayawa  suna dogara da kudaden da ake turo masu daga asusun tarayya domin wadannan kudade ba zasu isa su rika yiwa al’ummominsu ayyukan cigaba ba.

  A karshe ya bayyana cewa ya zama wajibi shugabannin kananan hukumomin, su tashi su nemo wasu hanyoyin da zasu rika samun kudade domin su rika yiwa al’ummominsu ayyukan cigaba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here