Gwamnonin Da Ke kin Shirin Ruga Na So A Ci Gaba Da rikici – Miyetti Allah

0
777

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN kungiyar Miyetti Allah na Najeriya ( MACBAN) reshen jihar Nasarawa, Alhaji Mahammad Huseni ya bayyana cewa duk gwamnan da yaki amincewa da shirin Gwamnatin Tarayya na gina wa makiyaya Ruga a jihohinsu toh yana neman a ci gaba da rikici.

Huseini ya fadi hakan ne a wata hira da yayi da manema labarai a Lafia, babbar birnin Nasarawa, inda yake karfafa cewa shirin Ruga a fadin jihohi 36 da ke kasar zai tabbatar da karshen rikici da ke tsakanin manoma da makiyaya.

Ya bukaci gwamnoni masu shakka da su bi sahun takwarorinsu wajen shiga cikin shirin don tabbatar da kawo karshen rikici dake aukuwa a jihohinsu.

A cewar shugaban kungiyan, a shirye yan Fulanin a jihar Nasarawa suke, sun kuma bada goyon baya ga shirin Gwamnatin Tarayya akan kaddamar da shirin, yayin da yake roko ga sauran kabilu masu tu nan in ana iya samun mumunar sakamako idan Ruga ta canja ra’ayi nan gaba.

Shugaban ya mika godiya ga Gwamnan jihar Injiniya Abdulahi Sule kan goyon baya da ya baiwa shirin Gwamnatin Tarayya a jihar.

A halin da ake ciki, bayan jingine shirin samar da rugar makiyaya da gwamnatin tarayya tayi a kwana-kwanan nan sakamakon cece-kuce da aka rika yi kan batun, Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautel Horre na Kasa, Alhaji Abdullahi Bodejo ya roki gwamnatin tarayya ta bawa makiyaya Dajin Sambisa.

Bodejo ya shaida cewa Fulani ba su bata neman a samar musu da ruga ba tun farko, ya dai ce ne kawai suna bukatar a samar musu da kayayakin da suke bukata ne domin su koma sabon wurin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here