Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 13 A Jihar Katsina

0
998
Daga Mustapha Imrana Abdullahi.
DARURUWAN mutane daga karamar hukumar Dan Musa da Kankara sun dauki gawarwakin mutane goma sha daya inda suka nufi fadar sarkin katsina domin nuna masa irin barnar da yan Bindiga suka yi masu.
Su dai yan bindigar sun bude wuta ne ga wadanda suka halarci kasuwar garin Mai Dabino da misalin karfe biyar da minti goma na yamma.
Sakamakon harin mutane da yawa sun tsorata lamarin da yasa da yawa suka ji rauni saboda halin firgicin da suka shiga.
Kamar yadda majiyarmu ta sabo cikakken rahoto masu dauke da gawarwakin sun kai su asibitin katsina kuma daga nan suka dauke su zuwa fadar sarkin katsina domin ayi masu sallar gawa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar katsina SP Gambo Isa, cewa ya yi an harbe mutane sha daya ne a kankara mutane biyu kuma a Mai Dabino.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here