A Jigawa : Gidaje 50 Sun Rushe, Mutane 200 Sun Rasa Matsugunnai

0
612
Daga Mustapha Imrana Abdullahi.
AMBALIYAR Ruwan ta rushe sama da gidaje 50 tare da raba mutane sama da 200 da matsugunnansu a Yalleman da Dakayyawa na Karamar Hukumar Kaugama a Jihar Jigawa.
Jami’in Hulda da Jama’a na Karamar Hukumar, Alhaji Fahad Muhammad, ne ya shaidawa manema labarai a Kaugama cewa, ambaliyar Ruwan ta faru ne sakamakon wani  Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka fara tun da misalin karfe hudu  na yammacin Litinin har zuwa karfe Goman na dare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here