Isah Ahmed, Daga Jos.
SHUGABAN majalisar malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari, da kada ya kuskura ya baiwa makiyansa mukamai a gwamnatinsa.
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi wannan kiran ne, a lokacin da yake gabatar da nasiha a masallacin ‘yan taya, da ke garin Jos a ranar juma’ar da ta gabata.
Ya kara da cewa sam bai kamata shugaba Buhari ya baiwa mutanen da suki a sake zabensa, karo na biyu mukamai ba.
Ya ce “babu shakka idan aka kuskura aka baiwa irin wadannan mutane mukamai a wannan gwamnati, zasu rusa gwamnatin.”
Har ila yau ya yi kira ga ‘yan majalisar dattawa da ‘yan majlisar wakilai da ‘yan majalisun jihohi su tsaya, wajen ganin an nada mutane na kwarai a nade naden da ake yi a kasar nan.
Ya ce bai kamata ‘yan majalisun su bari a nada mutanen da aka san barayi ne, a wuraren da suka ayi aiki a baya ba.
‘’Ayi kokari a zabo mana mutane managarta a nade naden da ake yi a gwamnatocin kasar nan, domin su taimaka wajen warware mana matsalolin da muke fuskanta a kasar nan’’.
Ya yi kira ga malaman addinin musulunci da malaman addinin kirista da sarakuna da ‘yan siyasa da sauran al’ummar kasar nan, su tashi tsaye wajen magance matsalar miyagun kwayoyin da ake shigowa da su kasar nan.
Ya ce maiyagun kwayoyi da ake shigowa da su kasar nan ne, suke jefa matasanmu cikin mummunan halin da suke ciki na aikata ta’addanci a kasar nan.
Daga nan ya yi kira ga maniyyata aikin hajin bana, idan suka isa kasa mai tsarki su yi abin da zai kara daga darajar Najeriya. Maimakon aikita laifaffukan da zasu bata sunan Najeriya.