Hayakin Janareto Ya Halaka Yara 2 A Katsina

0
794

Daga Mustapha Imrana Abdullahi.

GARIN birnin katsina ya shiga cikin wani mawuyacin halin firgici da dimauta sakamakon yadda hayakin Janareto ya yi sanadiyyar mutuwar yara biyu Yusuf da Dauda  a ranar Juma’a, yaran dukkansu yan shekaru sha takwas.

Kamar yadda majiyarmu ta labarta mana cewa an kunna janareton ne a ranar daren  Alhamis su kuma yaran suna cikin shago inda bacci ya kwashe su.

Kamar yadda shedan gani da Ido ya tabbtar mana cewa yaran sun kulle kansu ne a cikin shagon tare da Janareton a ciki kafin baccin ya kwashe su.

Shaidan gani da idon ya tabbatar mana da cewa shagon na wani  mai sayar da kayan Babura da motoci ne.

Shagon dai yana kan titin Yahaya Madaki ne a cikin birnin katsina.

Kuma tabbatattun bayanai sun shaida mana cewa man cikin Janareton ne ke haifar da wannan hayakin da ya yi sanadiyyar mutuwar yaran.

Wanda sakamakon hakan aka samu jami’an tsaron farin kaya na sibil difens Suka bambare kofar  Dakin inda aka tarar lamarin ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here