Cutar Ƙyanda Ta Kashe Yara 6 A Kaduna

0
4825

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

AKALLA rayukan yara shida ne suka salwanta, yayin da yara da dama ke cikin rashin lafiya mai tsanani a sakamakon barkewar cutar ƙyanda cikin kauyen Wusar dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Yara shidan da suka riga mu gidan gaskiya sun kasance cikin yara 30 da aka bayar da rahoton sun kamu da cutar ƙyanda da ta tsinke cikin kauyen Wusar tsawon watanni biyu da suka gabata.

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Balarabe, ta bayar da shaidar wannan lamari yayin da ta kai ziyayar gani da idanu da kuma janjantawa al’ummar kauyen Wusar.

Hajiya Hadiza ta alakanta bullar wannan muguwar cuta a yankin da gazawar iyaye wajen rashin tabbatar da an yiwa yaran su alluran riga kafi a lokutan da suka dace domin kariya da kuma yakar cututtuka masu kassara kananan yara.

Ta kuma bayyana rashin samun wadataccen abinci mai gina jiki da kuma rashin tsafta da suka haddasa annobar cututtuka masu janyo barazana ga lafiya da rayukan kananan yara a yankin.

Mataimakiyar gwamnan ta ja hankali tare da gargadin iyaye da su tabbatar da an yiwa yaran su alluran riga kafi a kan kari tare da bayar da muhimmancin a kan tsaftacce muhallai domin yakar cututtuka da kuma tsare lafiyar yaran su.

Hakazalika ta bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta shiga cikin lamarin cikin gaggawa domin gudun aukuwar hakan a lokuta na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here