Gwamnatin Filato Ta Dauki Nauyin Biyan Kudin Kujerun Hajji 630

0
556
Isah  Ahmed, Daga Jos.

GWAMNATIN Jihar Filato ta daukin nauyin biyawa alhazai kudin kujerun aikin hajjin bana,  guda 630.

Babban sakataren hukumar jin dadin alhazan ta jihar Filato, Barista Auwal Abdullahi ne ya bayyana haka, lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.

Barista Auwal ya bayyana cewa a bana alhazai guda 1200 ne, zasu tafi aikin hajji daga Jihar Filato kuma a cikin wadannan alhazai, gwamnatin ta Jihar Filato ta dauki nauyin biyawa alhazai kudaden kujeru guda 630, a ya yinda da jama’a suka biya sauran kudaden kujerun.

Ya kara da cewa wannan adadi ya nuna cewa a Jihar Filato ba a taba samun yawan alhazan da gwamnatin Jihar ta biyawa kudaden kujeru, kamar na wannan shekara ba.

Ya ce “gwamnatin Filato tayi dukkan abubuwan da suka kamata, don ganin alhazan Jihar sun ji dadin gudanar da aikin hajjin bana.”

Acewarsa, hukumar alhazan ta kammala dukkan shirye shiryen tafiyar alhazan  zuwa kasa mai tsarki don haka a ranar larabar nan mai zuwa alhazan Jihar Filato, zasu fara tashi zuwa kasa mai tsarki.

A karshe, barista Auwal, ya yi  kira ga maniyyatan  su kasance masu jin tsoran Allah, tare da bin abubuwan da shugabannin su suka umarce su wanda yin hakan zai sanya a sami nasara a wannan aikin hajji da za a gudana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here