APC Ta Lashe Zaben Cike Gurbi Na Dan Majalisar Dokokin Filato

  0
  599
  Mista Yakubu Sanda na jam’iyyar APC

  Isah Ahmed, Daga Jos.

  HUKUMAR zave mai zaman kanta ta kasa [INEC] ta bayyana cewa Yakubu Sanda na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben cike gurbi, na Dan majalisar dokokin Jihar Filato na mazabar Pengana, da ke Karamar Hukumar Bassa da aka gudanar, a ranar asabar din da ta gabata.

  Shi dai wannan zaben cike gurbi an gudanar da shi ne, sakamakon rasuwar Dan majalisar wannan mazaba, Honarabul Ezekiel Afon Bauda wanda ya rasu a lokacin da ake tsakiyar bikin murnar cin zabensa karo na biyu, a gidansa da ke garin Jos a zaben da ya gabata.

  Da yake bayyana sakamakon wannan zabe a cibiyar tattara sakamakon zaben da aka ajiye a Kwalegin gwamnati da ke garin Jingir, babban jami’in da ya tattara sakamakon zaben. Farfesa Noel Wanang ya bayyana cewa an gudanar wannan zabe, a rumfuna zave guda 127 da ke mazabu 7 na wannan mazaba ta Pengana.

  Ya ce a wannan zabe da aka fafata Yakubu Sanda na jam’iyyar APC ya sami kuru’u 9222, a yayinda Yakubu Busa Buji na jam’iyyar PDP ya sami kuru’u 7083. Don haka ya bayyana Yakubu Sanda na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe wannan zabe.

  Da yake zantawa da wakilinmu bayan bayyana sakamakon zaben, sabon Dan majalisar da aka zaba Mista Yakubu Sanda, ya bayyana matukar farin cikinsa ga al’ummar wannan mazaba, kan yadda suka fito suka zabe shi.

  Har’ila yau ya yabawa al’ummar mazabar kan yadda aka gudanar da wannan zabe lafiya batare da wata hayaniya ba.

  Ya bada tabbacin cewa zai yi iyakar kokarinsa wajen ganin gwamnati ta sharewa al’ummar mazabar koke kokensu.

  Akarshe, Ya yi kira ga wanda suka yi takara kan ya bashi goyan baya da hadin kai, domin ganin an ciyar da wannan mazaba da Jihar Filato gaba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here