Bai Halatta A Ci Bashi A Yi Layya Ba – Malam Auwal

0
963

Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba.

WATAN Zul-Haj wata ne wanda idan ya kama musulmi da Allah ya huwa ce masa, yake sayen abin yanka domin yayi laiya wanda ita Laiya dai sunna ce wadda ta samo asali tun lokacin Annabi Ibrahim A.S. da aka umarce shi cikin barcinsa daya yanka dan sa Isma’ail wanda hakan ya sanya Allah madaukakin sarki ya musanya shi da rago daga gidan Aljanna.

Wannan lokaci idan ya zagayo kowace shekara musulmi kan sayi abin da zasuyi laiya domin koyi da manzon Allah.

Sai dai yayin da wasu bayin Allah ke yin laiya domin kwadayin samun lada wasu kuma suna neman mayar da abin gasa ko kuma al’ada suce sai sunci bashi domin suyi laiya kada ta wuce su wanda a kan haka wakilinmu a Kuros Riba ya tattauna da limamin masallacin barikin ‘yan sandan kwantar da tarzoma dake kalaba wato Mopol 11. Kan shin ko ya halatta musulmi yaci bashi domin yayi laiya?

Malam Auwal AbdulKarim, limamin masallacin yace “ A’a laiya ba kamar zakkar kono take ba domin ita laiya ana yin tane a ranakun 10 ga wata 11 da 12 zuwa 13.

Don haka a wadan nan ranaku ne ake yin laiya amma ga duk wanda bai samu ya gabatar a wadannan ranakun ba, to sai yayi hakuri har sai Allah ya kaimu wata shekarar.

Malam Auwal AbdulKarim yaci gaba da cewa bai halatta ba don Annabi S.A.W Ya ce addini Yusrun wato sauki ne bai halatta ba tun da ba wajibi bane yana cikin sunna manzo S.A.W Wanda Allah ya hore masa
saboda haka ba wajibi bane idan bashi da abin laiya yace sai yaje ya rikito bashi don ya gabatar da laiya bayan wannan bai halatta ba, don ba gwaninta bane a addinin musulunci mutum ya ci bashi yayi laiya ko domin farantawa iyalan sa ko burge jama.a” .inji shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here