Allah Ya Kara Taimakon Jarumai Da Gora Na Yankin Unguwar Sanusi

0
375
Gwamna Nasiru El-Rufa'i na goyon bayan tsaro a kowane mataki

Daga Zubair Sada

CIKI da gaskiya wuka ba ta huda shi, haka masu iya magana na Hausa suke fadi, wanda ya yi daidai da abin da yake faruwa a halin yanzu a yankin Unguwar Sanusi, da ke gundumar Tudun Wada Kaduna a inda jaruman suke ta kokarin ganin sun tsaftace unguwarsu daga matasa bata-gari.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin wani karamin matashin yaro da ake kira Isma’il Hilal da ke Unguwar Sanusi Kaduna a inda yake maida martani kan matasan nan da suka kasa fahimtar su zauna lafiya su bar sace-sace da shaye-shaye a yankin, duk da yadda aka ba su damar zabar ayyukan yi wato sana’o’i ko kuma komawa ga karatun Musulunci da na boko wanda ‘yan kwamitin tsaron suka fitar a matsayin wasu daga hanyoyin bi don tsaftace zukatan matasan.

Ya ci gaba da cewa, ko shakka babu, ya zuwa yanzu matasan da suka gagara bin doka da oda, za su gamu da jaruman kungiyar ‘A Bi Doka A zauna Lafiya’. Ya ce za a kaddamar da kungiyar na wucin-gadi ranar jajibirin salla babba kafin a kaddamar da ita bayan salla. Ya ce masu hannu da shuni da ilahin malaman unguwar na masallatai da sarakuna da dattijai suna goyon bayan wannan tafiya, wanda hakan na nuni da samar da cikakkiyar nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here