Kuskuren Sadarwa: Sojoji Sun Kashe ‘Yan Sanda Uku A Taraba

0
521
Rabo Haladu Daga Kaduna
RUNDUNAR ‘yan sanda ta kasa ta zargi wasu sojojin kasar nan da hallaka jami’anta uku tare da raunata wasu bayan da sojojin suka bude wa wata tawagar ‘yan sandan wuta a Jihar Taraba.
Lamarin ya faru ne a kan hanyar Ibi zuwa Jalingo, kamar yanda wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar ta bayyana cewa tawagar ta masu kai daukin gaggawa ce ta Intelligence Response Team (IRT).
Sanarwar ta ce tawagar tana karkashin jagorancin Felix Adolije, mataimakin sufuritanda na ‘yan sanda, inda ta je jihar domin kama wani da ake kira Alhaji Hamisu, wanda ake zargi da cewa kasurgumin mai satar mutane ne.
Daga nan ne sai kawai wasu “sojoji na Najeriyar suka bude wa tawagar wuta ba kakkautawa”, kamar yadda sanarwar da ta fito daga kakakin rundunar ‘yan sandan ta kasa, Frank Mba, ta bayyana.
Sanarwar ta kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun kama mutumin ne za su kai shi hedikwatar ‘yan sanda ta jihar a Jalingo lokacin da sojojin suka bude musu wuta, duk kuwa da cikakkiyar shedar da ke nuna cewa suna kan aikinsu.
Sai dai rundunar sojin ta musanta zargin, tana mai cewa ta yi tsammanin ‘yan sandan tawaga ce ta masu satar mutane domin wasu mutane ne daga yankin suka nemi a kai musu dauki saboda masu satar jama’a sun kai musu hari.
A dalilin haka ne suka tsayar da mutanen da ke tafiya a wata motar Bas amma suka ki tsayawa, dalilin da ya sa suka bude musu wuta.
Sai daga baya ne daya daga cikin wadanda suka tsira ya shaida musu cewa su ‘yan sanda ne daga Abuja, kuma an turo su ne domin gudanar da wani aiki na musamman kan masu satar mutane.
Bayan ‘yan sandan, lamarin ya kuma rutsa da ran wani farar hula, da sufeto da kuma wasu ‘yan sandan biyu masu mukamin saja, yayin da wasu ‘yan sandan kuma da ba a bayyana yawansu ba suka samu raunuka.
Sanarwar ta ce bayan nan ne sai sojojin suka “kubutar da wanda ake zargin”, abin da ya sa ya tsere, har yanzu ba a san inda yake ba.
‘Yan sandan suna zargin mutumin, Alhaji Hamisu da kasancewa kasurgumin mai satar mutane, da suka dade suna nema saboda hannu a sace-sacen jama’a ciki har da sace wani dan kasuwa mai harkar mai da aka yi kwanan nan a jihar ta Taraba.
Dan kasuwar mai sayar da mai wanda ba a bayyana sunansa ba a sanarwar, an ce sai da ya biya Naira Miliyan 100 aka sako shi.
Tuni aka tura wani mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda domin tsara yadda za a yi wa wadanda aka jikkata magani, yayin da kuma aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a asibiti.
Shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa Muhammad Adamu ya bayar da umarnin gudanar da binciken gaggawa kan lamarin, in ji kakakin rundunar ta kasa Mista Frank Mba, mai mukamin mataimakin kwaminishinan ‘yan sanda

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here