KASHI 30 CIKIN 100 NA MALUMAN MAKARANTUN YOBE BA SU DA KWAREWAR AIKIN KOYARWA…Inji Farfesa Daura

0
418
SANI GAZAS CHINADE,DAGA DAMATURU
AN bayyana cewar, kashi 30 daga cikin 100 na Maluman makarantun Jihar
Yobe ba su da kwarewar aikin koyarwa.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga shugaban kwamitin da Gwamnan Jihar
Yobe Alhaji Mai Mala Buni ya nada dangane da dokar ta-baci a kan
harkokin ilimi Farfesa  Mala M. Daura yayin da yake mika kundin
rahoton aikin kwamitinsu da suka kammala ga Gwamnan a gidan gwamnatin
Jihar da ke garin Damaturu.
Farfesa Mala M. Daura ya kara da cewar cikin aikin da kwamitinsu da ke
kunshe da hanshakan masu ruwa da tsaki na harkokin ilimi a jihar ya gudanar sun
gano cewar, akalla kashi 30 cikin 100 na Maluman makarantun jihar ba su
da kwarewar aiki inda ala tilas sai gwamnatin jihar ta dauki matakin
gaggawa musamman wajen kokarin daukar matakin sake horar da wadannan
malamai don ganin an kai ga nasarar cimma wannan manufa.
Ya kara da cewa, baya ga rashin kwarewar wasu malaman har ila yau kuma
da akalla kashi 70 daga cikin 100 na daliban jihar daga Firamare zuwa
sakandare duka suna zaune ne a kasa ba tare da abubuwan zama ba, wanda
kuwa hakan kan kawo nakasu a harkokin koyo da koyarwa.
Daga nan sai ya tabbatar da cewar lalle rikicin Boko Haram da jihar ta yi
fama da shi tsawon shekaru 10 ya yi matukar kawo koma baya ga harkokin
ilimin jihar.
Don haka ne shugaban kwamiti ya kara ba da shawara ga gwamnatin jihar
da ta samar da makarantun kimiyya da fasaha na musamman ga kowace
shiyyar mazabar majalisar dattijai uku da ke jihar kana ta kuma nemi
tallafi daga kungiyoyin ba da tallafi na duniya don kawo musu dauki da
sauran dabaru.
Da yake karbar ayyukan wannan kwamiti Gwamnan jihar Alhaji Mai Mala
Buni ya gode wa mambobin wannan kwamiti dangane da yadda suka gudanar
da wannan aiki nasu kana ya ba su tabbacin cewar in Allah ya so
gwamnatin za ta yi amfani da shawarwarin da suka bayar yadda ya kamata.
Don haka nan take Gwamnan ya ba da umarni ga sakataren riko na
gwamnatin jihar Alhaji Baba Malam Wali da ya gaggauta tsara yadda za a
yi amfani da shawarwarin da wannan kwamiti ya bayar don ganin an kai
ga nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here