Ana Ci Gaba Da Fafutukar Neman Sakin Dadiyata

0
435
Rabo Haladu Daga Kaduna
KIMANN mako guda kenan ‘yan Najeriya ke ta kiraye-kirayen a sako wani matashi mai tashe a shafukan sadarwa na zamani, wanda ya yi batan dabo a makon jiya.
Kiraye-kirayen a sako Abubakar Idris, wanda aka fi sani a kafafen na sada zumunta da suna Dadiyata, sun biyo bayan zargin da jama’a suka yi na cewa jami’an tsaron farin kaya na DSS suka kama shi, saboda yadda yake sukar manufofin gwamnatin tarayya da ta jihar Kano. To amma jami’an tsaro sun ce ba su suka kama shi ba.
Shi dai Dadiyata mai bin akidar Kwankwasiyya ne wanda ke biyayya sau-da-kafa ga tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma tsohon dan majalisar dattawa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Shafinsa na Twitter cike yake da hotunansa sanye da jar hula, wadda ita ce babbar alamar kungiyar ta Kwankwasiyya.
Mai dakin matashin, Khadija Idris Dadiyata ta shaida wa manema labarai cewa abin ya faru ne a ranar Alhamis bayan karfe 1:00 na dare a gidansu da ke Barnawa a jihar Kaduna.
“Bayan ya dawo daga tafiya ne ya shigo gida yana kokarin kulle kofa sai wasu suka shigo suka far masa,” in ji Khadija.
“Yana tsaka da yin waya ne kawai sai na ji kara. Ina daga labule sai na ga wasu mutum biyu suna kokawa da shi, amma ba zan iya tabbatar wa ba ko bindiga ce a hannun daya daga cikinsu.”
Ta kara da cewa ba ta iya ganin fuskarsu ba, saboda haka ba za ta iya cewa ko su wane ne ba.
Wannan wallafar wani ce a Twitter, inda yake cewa an yi amanna jami’an tsaro ne suka yi awon gaba da matashin.
Wane ne ya kama shi?
Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf dai yana ganin hukumar tsaron farin kaya ta DSS ce ta kama matashin.
Kakakin sa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya shaida wa manema labarai cewa sun yi amanna cewa jami’an tsaron farin kayan ne suka kama shi.
Ya ce haka suka yi dangane da kama Salisu Hotoro, inda da farko suka musanta cewa ba su suka kama shi, amma ya ce daga baya sai suka ce za su kai shi kotu.
Manema labarai sun yi yunkurin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda ta kasa Frank Mba, sai dai ya ce ba shi da masaniya kan labarin, kamar yadda ya bayyana ta wayar salula.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar DSS sai dai ya ce a ba shi lokaci zai ba da amsa, amma har lokacin wallafa wannan labarin bai bayar da amsa ba.
Sai dai jaridar Daily Nigerian wadda ake bugawa a Intanet ta ruwaito rundunar a baya tana musanta zargin cewa Dadiyata yana hannunta.
“Babu wani mai suna Abubakar Idris Dadiyata a hannunmu. Ba mu kama shi ba kuma babu wani abu mai kama da haka da ya faru,” in ji rundunar SSS ta jihar Kaduna a rahoton Daily Nigerian.
Jaridar ta kara da cewa ‘yan sanda a Jihar Kaduna su ma sun ce ba su da hannu a batansa.
Tun bayan batan na sa dai, an kaddamar da kiraye-kiraye da dama a kafofin sada zumunta na ganin an sako shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here