A Kara Yi Wa Kasar Nan Addu’o’i Na Samun Zaman Lafiya-Inji Usman Dan Gwari

0
425

JABIRU A HASSAN,Daga  Kano

WANI dan  kasuwa kuma jigo a jam’iyyar APC Alhaji Usman Dan Gwari ya bukaci ‘yan Nijeriya da su kara yi wa kasar nan addu’oi na musamman domin ci gaba da samun wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bunkasar tattalin arziki.

Ya yi wannan tsokaci ne a ganawar su da wakilinmu dangane da abubuwan da ke faruwa a kasar nan, inda ya sanar da cewa yawaita addu’a zai taimaka a sami kwanciyar hankali da zaman lafiya a wannan kasa ganin cewa yanzu al’amura sun kara tabarbarewa ta fuskar tsaro a wasu sassan Nijeriya.

Usman Dan Gwari ya kara da cewa dukkanin mabiya addinai biyu na kasar nan sun yarda  cewa addu’a ita ce maganin duk wani abu da ka iya jefa kasa cikin rudani da rashin tabbas, don haka ya shawarci gwamnatin tarayya da na jihohi da su himmatu wajen shirya tarurrukan addu’o’i na musamman domin neman kariya daga Allah Madaukakin Sarki.

Sannan ya bukaci a gudanar da wani bincike na musamman kan yadda ake yawan safarar shanu daga jihohin da suke fama da rikice-rikice zuwa kudanci duk da cewa babu harkokin kasuwanci a wadannan yankuna amma ake  safarar dabbobi musamman shanu a kowace rana.

A karshe, dan kasuwar ya yi fatan alheri ga al’umar musulmin duniya bisa sake zagayowar babbar sallah, tare da fatan Allah ya dawo da alhazanmu gida lafiya cikin yardar Ubangiji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here