Kocin Kwallon Guragu Ya Bai Wa Gwamnati Shawarar Share Bara A Tituna

  0
  669
  MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga  kalaba
  MATUKAR gwamnati na so ta magance yawon barace-barace da take kokawa da shi ga masu larurar nakasa a gabobin jinkin su suke yi musamman a Arewacin kasa da kuma masu kwarara zuwa sauran sassan kasa to, dole ta gina wuraren wasannin motsa jiki da masu larurar za su rika zuwa suna yin wasanni a matsayin sana’a
  Sani Ali Sale shugaban kungiyar wasan kwallon guragu dake jihar Kuros Riba ya fadi haka a zantawarsu da wakilinmu a Kalaba.
  Ya ce matukar gwamnati da gaske take yi kamata ya yi ta bubbude wuraren wasannin motsa jiki da kuma na koyon sana’o’in hannu musamman a Arewa domin su koya amma matukar ba hakan aka yi ba zai yi wuya mafarkin hana bara ko mabarata yin bara ba zai cimma nasara ba.
  Shugaban wanda aka fi sani da suna SAS yaci gaba da cewa “ A yanzun nan idan gwamnati ta kula da wasannin motsa jiki musamman na masu larurar nakasa za su hakura da dan abin da suke samu su tsaya wuri guda ba sai sun je sun yi bara ba saboda sun san cewa dai ko ba komai akwai dan tallafin da za su rika samu.”inji shi.
  Ya kara da cewa gaskiya kam za a samu sauin barace-barace, “na biyu kuma ko ba bangaren wasan ba idan akwai cibiyoyin koyar da sana’a idan aka yi su a ko ina musamman  a Arewa suna zuwa suna koyo za su samu abin da za su ci gaba da dogara da kansu”.
  An yi wasan sada zumunci tsakanin kungiyar wasan kwallon guragu ta jihar Ribas  da takwararta ta Kuros Riba an tashi wasan canjaras babu wata kungiya da ta yi galaba
  kan ‘yar uwarta. Wasan ana shirya shi tsakaninsu kowace shekara idan bukukuwan salla
  karama da babba ya zo ranar Litinin da ta gabata aka gudanar da wasan a
  harabar filin da suka saba yi da ke layin Mary Slessor a Kalaba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here