MASU SAYAR DA RAGUNA SUN KOKA DA FADUWAR FARASHI DA SUKA YI A KUROS RIBA2

0
582
Misbahu Muhammad Mai Sana'ar Sayar da Raguna
MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga kalaba
KASUWAR salla da akaci da  masu sana’ar sayar da dabbobi raguna da suka kawo talla jihar Kuros Riba sun ce cinikin na wannan shekara babu riba sai ma faduwa ya jawo musu Musbahu Muhammad Jigawa daya daga cikin ‘yan kasuwar da suka kawo tallar sayar sayar da raguna tun daga jigawa zuwa Kuros Riba ne ya bayyana wa wakilinmu na Kudanci haka.
Ya ce “An samu matsalar kasuwa ragon da a sari muka sawo shi Naira dubu arba’in an sayar da shi Naira dubu talatin da biyu zuwa da uku , mun danganta hakan da kamar yadda muka samu mutane a gari suna kukan ba kudi-ba-kudi shi muke ganin ya haddasa haka”.inji shi.
Ya ci gaba da cewa su tunanin su rashin kudin da jama’a ke kokawa ya jawo musu amma “mu mun san daga Allah ne dole kowa ne dan kasuwa ya san samu ya san da rashi yana tattare da wata rana ya samu wata rana kuma zai iya rasawa ”.
Mahammad Jigawa yace a kalla raguna “kamar ashirin da hudu,daga cikin dari da arba’in da  muka sayo domin mu sayar a ci riba muka sayar da su faduwa”. Sai dai cinikin shekarar da ta gabata ya sha banban da na wannan shekara saboda “kamar yadda aka yi kasuwa bara mu bana bata zame mana haka ba, saboda mun ga ta yi kasa a kan bara shi ya sa ma muka fara tunanin rage yawan dabbobin da muke kawowa talla Kalaba sayarwa shekara mai zuwa saboda anji jiki kasuwar ta bana”.Kimanin raguna dari da arba’in suka kawo sayarwa Kalaba amma sauran sai bisa faduwa suka rika sayar da ‘yan ragowar.
Daga cikin raguna ashirin da biyar da suka rage ba a saya ba ala-tilas suka karyar da farashin suka sayar domin su koma gida a sake shirin kasuwar badi ba wai a ci riba ko faduwa ba .
Wata matsala da dan kasuwar ya koka da  suke fuskanta ya ce sun fuskanci matsaloli a hanya tun daga Abakalake jihar Ebonyi zuwa nan Kuros Riba,wajen masu karbar kudin jangali da kula da wucewar ababen hawa a wannan hanya sun rika biyan masu karbar kudin jangali Naira dubu goma-goma kowane shinge wasu shingayen ma sai da suka rika
biyan dubu hudu wani kuma dubu biyar da suka shigo jihar Kuros Riba,“wuri daya ma mun yi jangali guda hudu a kowane shingen jami’an tsaro da na masu karbar jangali tun daga jihar Jigawa zuwa kudancin kasar nan suna kashe kudi kimanin Naira dubu dari da talatin kafin su isa kasuwar su da za su sauke kaya.
Karshe ya bukaci gwamnati ta duba lamarin wadan da take ajiyewa kan hanya suna duba ababen hawa domin wasun su lamarin nasu sai dai addu’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here