MUN KAFA KUNGIYAR ZAMFARA SOLIDARITY DOMIN TAIMAKON KANMU – Aminu Riyo

0
572
Ga wasu daga shugabannin kungiyar ZSA da ke Kalaba
MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba
‘YAN asalin jihar Zamfara mazauna yankin kudu maso kudancin kasar nan mazauna jihar Kuros Riba sun kafa kungiyar yi wa Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle mubaya’a mai suna Zamfara Solidarity Association sakamakon nasara da ya samu cikin kankanen lokaci na dawo da martabar jihar tun daga  karbar ragamar mulkin jihar daga hannun tsohon Gwamnan jihar an samu nasarar samar da zaman lafiya da kuma ‘yan bindiga da suka hana wani sashe na jihar sakat suna ta tuba suna mika makamansu ya sanya su ma suka kafa kungiyar domin mara wa Gwamnan baya ya ci gaba da samun nasara .
Da yake yi wa wakilinmu na Kudanci karin haske game da dalilan su na kafa kungiyar shugaban kungiyar a jihar Kuros Riba Alhaji Aminu Bello Muhammad wanda aka fi sani da suna Aminu Riyo ya ce “Abin da ya jawo hankalinmu muka kafa ita wannan kungiya shi ne mu mazauna Kurmi mun lura cikin kankanen lokaci gwamnatin Matawalle tana samun nasarar dawo da martabar jihar Zamfara wajen samar da zaman lafiya da tsaro kuma
yana dawo da martabar jihar a idon duniya sannan kamar mu da ke nan Kalaba jihar Kuros Riba baya ga mubaya’a ga gwamnatin muna taimakon junanmu wadanda mafi yawancimu mu ‘yan kasuwa ne idan Allah ya jarabci wani dan uwanmu da wata matsala za mu taimaka masa da karfin aljihunmu bakin gwargwado domin mu ga ya samu waraka ko kuma sauki a wannan jarabta da Allah ya yi masa “inji shi.
Haka nan kuma bayan taimaka wa juna muna nan muna yunkurin daga nan zaune mu ‘yan asalin jihar mazauna jihohin kudu maso kudu mu rika taimaka wa gwamnati da shawarwari , da kuma adduo’i.
shugaban kungiyar zamfara solidarity Association din ya ce babban kalubalen da suke fuskanta shi ne wasu daga cikin al’ummar jihar mazauna kudanci kamar ba su fahimci manufar kafa kungiyar ba “amma muna nan muna bakin kokari mu ga mun fahimtar da su domin gane manufarmu ta alheri ce da kuma ci gaban jiharmu da duk wani dan asalin jihar mazaunin wajen jihar”.
Haka nan kuma Aminu Riyo ya ce za su hada karfi da karfe da kafafen yada labarai na kasar nan domin yayata manufofinsu domin sauran ‘yan asalin jihar da ke sauran sassan kasa su zo a gudu tare a tsira tare.
Karshe shugaban kungiyar ya yi  fatan al’ummar jihar za su ba gwamnatin Bello Matawallen Maradun da ‘yan majalisar dokoki ta kasa,da Kabiru Garba Marafa bisa jajircewar su wajen dawo da martabar jihar hakika cikin dan kankanen lokaci mun ga yadda aka samu nasarar dawo da martabar jihar da saita ta kan zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here