Adam Zango Ya Yi Hadari A Nijar

0
645
Rabo Haladu Daga Kaduna
FITACCEN jarumin fina-finan Hausa na Kannywood kuma mawaki, Adam A. Zango, ya yi hatsarin mota.
Zango yana tafiya ne a kan hanyarsa ta dawowa daga Jamhuriyar Nijar tare da wasu abokansa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Sai dai jarumin ya ce “Allah Ya kare su, domin hadarin ya tsaya ne kawai a kan motar da suke tafiya a ciki”.
Zango yana yawan yin tafiye-tafiye musamman a lokutan bukukuwan sallah, inda ake gayyatarsa domin yin casu. Manema labarai sun yi kokarin tuntubar A Zango domin neman karin bayani kan lamarin amma bai amsa wayar ba kawo yanzu.
Amma bayanai a shafinsa na Instagram sun nuna cewa ya je Nyame, babban birnin Nijar, domin yin wasan sallah.
Masu lura da al’amura na alakanta hakan da rashin kyawon hanyoyi da kuma tukin ganganci daga bangaren wasu matafiyan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here